
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A ranar Talata Antoni Janar kuma Kwamishinan Shari’ar Jihar Kano, Abdulkarim Kabiru Maude (SAN) ya kai ziyarar aiki ga Kwamishinan ‘yan sanda, Ibrahim Adamu Bakori domin duba matakin binciken al’amarin kisan gillar da aka yi wa wata uwa da ‘ya’yanta shida a Unguwar Ɗorayi Charanchi da ke jihar.
An gudanar da zaman ne da ya haɗa da ƙwararrun jami’ai daga rundunar ‘yan sandan Kano da wasu daga sauran hukumomin tsaro da sashen bincike a ofishin kwamishinan domin tabbatar da amfani da dabaru wajen aiki akan iftila’in.
Daga cikin manufar haka akwai ƙoƙarin gurfanar da waɗanda ake tuhuma a kotu akan lokaci da zartar da hukuncin da ya dace akansu ba tare da ɓata lokaci ba.
A ranar Asabar ne aka samu wasu ɓata-gari a Unguwar Charanch suka shiga wani gida inda suka halaka wata mata mai suna Fatima Abubakar da ‘ya’yanta guda shida a wani yanayi na gilla, lamarin da ya tada hankalin al’umma musamman a arewacin Nijeriya.
Akan haka ne jami’an tsaro suka bazama wajen binciken, wanda a sanadiyyar haka suka kama mutane uku da ake zargi da hannu a ciki waɗanda a yanzu suna hannun hukumar.
Kwamishinan shari’ar ya yi nuni da muhimmanci aiki kafaɗa-da-kafaɗa da jami’an tsaro musamman akan irin wannan al’amari da ke da buƙatar zurfafa bincike da nuna ƙwarewar aiki.
Ya kuma tabbatar wa rundunar ‘yan sandan cewa ma’aikatarsu a shirye take ta bayar da dukkan haɗin kan da ake buƙata wajen ganin an yi nasara a shari’ar lamarin.
Kazalika, Maude ya tabbatar wa al’umma cewa gwamnatin jihar tana aiki tuƙuru wajen tabbatar an yi wa iyalan adalci, kamar yadda Mai taimaka wa antonin akan lamuran yaɗa labarai, Abubakar Tijjani Ibrahim ya bayyana a wata takarda.
