
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Aƙalla jami’an soji guda biyar da ɗan sanda ɗaya ne suka rasu a ranar Litinin, sakamakon wata kwanton ɓauna da ‘yan ta’adda suka yi akan jami’an atisayen FANSAR YAMMA a babbar hanyar Bingi zuwa Kekun da Waje zuwa Gusau da ke Jihar Zamfara.
Rahotanni sun nuna cewa mummunan al’amarin ya faru ne lokacin dakarun suke dawowa daga wasu atisaye da suka ƙaddamar a tsakanin ranakun 17 da 19 ga watan Junairu a ƙananan hukumomin Birnin Magaji da Anka ina suka yi gagarumar nasara ta tarwatsa sansanonin ‘yan ta’adda.
Da yake tabbatar da al’amarin a wani saƙo ta kafar X ranar Talata, jami’in hulɗa da jama’a na FANSAR YAMMA, Kyaftin David Adewusi ya ce da fari jami’an sun kai farmaki da kwanton ɓauna akan ‘yan ta’adda, wanda ya kai ga kama waɗanda ake zargi da ta’addanci da ƙwato wasu muggan makamai.
A cewarsa, daga cikin waɗanda aka kaman akwai Isiya Kwakwatawa, Ibrahim Ɗan Musulu da Makau Lamba.
Ya ƙara da cewa, an halaka ‘yan ta’adda guda huɗu yayin da da dama suka tsere ɗauke da munanan raunuka zuwa dazukan da ke kewayen yankunan.
Ababen da aka ƙwato sun haɗa da bindigar PKT, AK-47 guda biyar da mazubin alburusansu uku, alburusan 7.62mm masu yawa, na’urorin sadarwa na Baofeng da kuma babura uku.
Saidai, komawarsu ta samu tsaiko yayin da wasu daga cikin ‘yan ta’addar suka yi wa dakarun sanɗa a yankin Gidan Wagni yayin da suka nufi Kekun Waje.
Akan haka ne suka aika wasu dakaru domin mayar da martani akan ‘yan ta’addar, lamarin da ya sa suka ja da baya sakamakon fin ƙarfi da dakarun suka nuna.
