Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
“Mata Sune ƙashin bayan al’umma. Inganta Rayuwarsu daidai yake da inganta rayuwar al’umma”Inji Raɗɗa
Gwamna ya bayyana hakanne yayin ƙaddamar da babban shirin tallafa wa mata ’yan kasuwa guda 14,450 a Jihar Katsina.
A wani muhimmin mataki na bunƙasa tattalin arzikin jihar Dikko Raɗɗa ya ƙaddamar da wani gagarumin shirin tallafa wa mata ’yan kasuwa 14,450 a faɗin jihar don dogaro da kansu.
An tsara shirin ne domin tallafa wa mata da ke gudanar da sana’o’i daban-daban kamar sana’ar hannu, kasuwanci, noma, ɗinki, rini, sarrafa abinci da sauransu, waɗanda da dama daga cikinsu su ne ginshiƙin tattalin arzikin iyalansu da alummarsu.
Gwamna Raɗɗa ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa na fifita manufofin da ke tallafa wa mata, inda ya bayyana shirin a matsayin zuba jari a kan mata, zaman lafiya da bunƙasar tattalin arziki mai ɗorewa.
Ya nuna cewa ƙarfafa mata yana ƙarfafa iyalai, samar da wadatar abinci da kuma kawo ci gaban al’umma.
A jawabinta, matar gwamnan Hajiya Zulaihat Dikko Raɗɗa ta bayyana shirin a matsayin hanya mafi sauri wajen magance matsaloli a cikin alumma tare da kira ga mata da suyi amfani da tallafin wajen dogaro da kansu.
Kwamishinan harkokin mata, Hajiya Aisha Aminu Malumfashi, ta yaba wa Gwamnan bisa fifita shigar mata cikin harkokin tattalin arziki, tana mai bayyana shirin a matsayin mataki wanda ya dace da lokaci wanda zai magance manyan ƙalubalen da mata ’yan kasuwa ke fuskanta.
Ta ƙara da cewa shirin ya yi daidai da manufar ma’aikatarta ta ƙarfafa dogaro da kai, mutunci da walwalar mata a faɗin jihar.
Haka shima kwamishinan ƙananan hukumomi da masarautu, Hon Bishir Tanimu, ya bayyana cewa shirin yana da tushe a matakin al’umma, inda ya tabbatar da cewa ya shafi dukkan ƙananan hukumomi ba tare da wariya ba. Ya kuma jaddada shirye-shiryen ƙananan hukumomi na sa ido da tabbatar da aiwatar da shirin yadda ya kamata a matakin mazaɓu.
Kwamishinan matasa da wasanni, Engr Surajo Yazeed Abukur shima ya bayyana cewa shirin zai haifar da tasiri mai zurfi a tsakanin al’umma, musamman ga matasa, domin ƙarfafa mata na taimakawa kwanciyar hankali a gida, tarbiyyar yara da inganta haɗin kan al’umma.
Ya ce mata masu ƙarfin tattalin arziki na taka muhimmiyar rawa wajen tallafa wa ilimi, koyon sana’o’i da jagoranci ga matasa.
Mai Kula da shirin ci gaban al’umma (CDP), Dr Kamal, ya bayyana shirin a matsayin misali na mulki da ya maida hankali kan jama’a, inda ya bayyana rawar da jami’an CDP sun taka wajen wayar da kai, tantancewa, sa ido da bin diddigi domin tabbatar da shirin ya haifar da sakamako mai ɗorewa.
Shugaban kwamitin majalisar dokoki kan harkokin mata, Hon Albaba ya yaba da shirin, yana mai bayyana shi a matsayin babbar nasara, tare da tabbatar da goyon bayan majalisa wajen samar da dokoki da sa ido da za su bunƙasa ƙarfafa tattalin arzikin mata.
Haka zalika, shugaban ALGON na jihar, Hon Rabo Tambaya ya yaba da shirin, yana mai bayyana shi a matsayin kyakkyawan misali na haɗin kai tsakanin gwamnatin jiha da ƙananan hukumomi. Ya tabbatar da cewa ƙananan hukumomi za su ci gaba da bayar da goyon baya da sa ido domin cimma manufar shirin.
