
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Manchester United ta ce ɗan wasanta na tsakiya Casemiro zai bar ƙungiyar a lokacin da kwantiraginsa ya ƙare a ƙarshen kakar wasan bana.
Ɗan wasan mai shekaru 33 ya koma United ne daga ƙungiyar Real Madrid akan kuɗi Fam miliyan 70 a shekarar 2022, wanda a yanzu ya buga mata jimillar wasanni 146.
Haka kuma, shi ne wanda ya zura ƙwallon farko a wasan ƙarshe na gasar Carabao Cup na 2023 da Manchester ta doke Newcastle United, inda kuma a lokacin ne United ta ƙare a mataki na uku a Gasar Premier League.
A yanzu dai ƙungiyar ba ta da shirin tsawaita zaman ɗan wasan, mai karɓar albashin Fam 375,000 a kowane mako a United kasancewar kwalliya ta gaza biyan kuɗin sabulu.
Casemiro dai ya sha fuskantar suka na zamansa a ƙungiyar daga masu sharhi akan harkar ƙwallon ƙafa, musamman bisa la’akari da rashin nasarar United akai-akai da girman adadin albashin da yake karɓa.
