
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sabon mai horar da ‘yan wasan Real Madrid, Alvaro Arbeloa ya bayyana aniyarsa ta cigaba da jan ragamar ƙungiyar a kakar wasa ta gaba.
A cewar wani rahoto da El Nacional ta fitar, Arbeloa ya kuma shawarci ɗan wasan baya, Alexander-Arnold na ƙasar Ingila da ya shirya barin ƙungiyar kasancewar ba ya daga cikin ‘yan wasan da kocin yake shirin tafiya da su.
Haka na zuwa ne ƙasa da kwanaki 14 da Arbeloa ya kama jagorancin ƙungiyar bayan Madrid ta sallami Xabi Alonso a muƙamin.
Duk da cewa da fari ana ganin naɗin Arbeloa a matsayin na riƙo, hakan bai sa ya yi ƙasa a gwiwa ba wajen amfani da ikonsa na jagorantar gina tawagar ‘yan wasan ƙungiyar.
Ana ganin matakin ya samu ne sakamakon rashin gamsuwa da gudumawa da ɗan wasan ke bai wa ƙungiyar daga ɓangaren Arbeloa.
Alexander-Arnold mai shekaru 27 shi ne ɗan wasa na farko da tsohon koci, Alonso ya gayyato cikin ƙungiyar daga Liverpool a kakar bara.
Ɗan wasan ya fuskanci ƙalubalen samun rauni akai-akai, wanda ya sa a iya wasanni 11 kacal aka gan shi a dukkan gasar da ƙungiyar ke bugawa.
Masu sharhi na ganin ɗaukar matakin akan ɗan wasa irin wannan kuskure da rashin ƙwarewa ne musamman bisa la’akari da ƙwarewarsa da kuma tsawon lokaci da aka ɗauka ana farautarsa a matsayin wanda zai maye gurbin Dani Carvajal a Madrid.
