Kofin Ƙalubale na Turai: Ƙungiyoyin Ingila sun tsallake zuwa zagaye na gaba yayin da Madrid ta samu cikas

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyoyin ƙasar Ingila guda biyar sun yi nasarar hayewa zuwa zagaye na gaba a gasar kofin zakarun Nahiyar Turai daga zangon farko na kakar 2025/2026.

Newcastle united ta shiga sahun waɗanda za su buga wasan ƙalubale gabanin zagayen ‘yan 16, wato ‘Play Offs’.

Haka ma ƙungiyar Real Madrid, wadda ta lashe kofin har sau 15 a tarihinta, ta samu tsaiko na kai wa zangon kai-tsaye bayan da Benfica ta ƙasar Portugal da José Mourinho ke jagoranta ta lallasa ta da ci 4 da 2, inda mai tsaron gidanta Anatoliy Trubin ya zura ƙwallo ƙarshe a ragar Madrid a minti na 98.

Wannan rashin nasara ya haifar wa Madrid cikas na shiga sahun takwas ɗin farko da suka haye zagaye na gaba kai-tsaye bayan ƙare wasan da ‘yan wasa tara sakamakon bai wa Raul Asencio da Rodrygo katin sallama.

A yanzu haka, Madrid za ta kara da Benfica ko kuma tsohuwar ƙungiyar Mourinho, wato Inter Milan a rukunin play off.

Ita ma Newcastle ta gaza kai wa zangon ‘yan 16 ne kai-tsaye bayan da PSG ta riƙe ta kunnen doki inda aka tashi 1 da 1 a tsakaninsu, lamarin da ke nuna za ta kara da ɗaya daga cikin ƙungiyoyin da suke a sahu ɗaya.

Ga yadda sakamakon wasannin ƙarshen zangon farkon suka kasance:
Ajax 1-2 Olympiacos
Arsenal 3-2 Kairat Almaty
Athletic Club 2-3 Sporting CP
Atletico Madrid 1-2 Bodø/Glimt
Barcelona 4-1 Copenhagen
Bayer Leverkusen 3-0 Villarreal
Benfica 4-2 Real Madrid
Borussia Dortmund 0-2 Inter
Club Brugge 3-0 Marseille
Eintracht Frankfurt 0-2 Tottenham
Liverpool 6-0 Qarabag
Man City 2-0 Galatasaray
Monaco 0-0 Juventus
Napoli 2-3 Chelsea
Pafos 4-1 Slavia Prague
Paris Saint-Germain 1-1 Newcastle
PSV Eindhoven 1-2 Bayern Munich
Union SG 1-0 Atalanta.

By Babaji