
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Hukumar zaɓe ta ƙasa, INEC, ta ce ta kammala shirye-shiryen gudanar da zaɓen cike gurbi na Majalisar Dokokin Jihar Kano a mazaɓun ƙananan hukumomin Birni da Ungoggo.
Hakan na zuwa ne sakamakon rasuwar ‘yan majalisa biyu da ke wakiltar mazaɓun a watan Disamba.
Hukumar, ta bakin shugabanta na Kano, Amb. Abdullahi Zango, ta ce jam’iyyu goma ne suka tsayar da ‘yan takara a zaɓen.
Ya ce, tun suka karɓi sunayen jam’iyyun waɗanda suka cika duk ƙa’idoji da sharuɗɗan da doka ta tanada.
INEC ta bayyana cewa ana sa ran gudanar da zaɓen cike gurbin a ranar 21 ga watan Faburairu.
Jam’iyyun da za su fafata a zaɓen sun haɗa da APGA, APC, ADP, AAC, PRP, LP, GP, AC da NNPP.
A halin yanzu, INEC ta tura masu sanya ido domin bibiyar zaɓukan fidda gwani na jam’iyyun, da nufin tabbatar da an gudanar da su cikin gaskiya da bin doka.
