NELFUND ta ƙaryata rahotannin bogi kan fara karɓar bashin lamunin ɗalibai

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Hukumar Ba da Lamunin Ilimi ta Nijeriya (NELFUND) ta fito ƙarara ta ƙaryata rahotannin da ke yawo a kafafen sada zumunta da wasu kafafen yaɗa labarai, waɗanda ke iƙirarin cewa an umurci zaliban da suka amfana da shirin lamunin ɗalibai da su fara biyan bashin.

A cikin wata sanarwa da ta fitar a ranar Lahadi, wacce Daraktar Sadarwa ta Dabaru, Oseyemi Oluwatuyi ta sanya wa hannu, hukumar ta bayyana waɗannan rahotanni a matsayin ƙarya, ruɗani da kuma marasa tushe.

Sanarwar ta ce, wannan bayani ya biyo bayan wata sanarwa da Shugaban Jami’ar Benin (UNIBEN), Farfesa Edoba Bright Omoregie (SAN) ya fitar, inda ya nesanta jami’ar da wata takarda da ake yaɗawa wacce ke ɗauke da matakan biyan bashin lamunin NELFUND.

Jami’ar ta tabbatar da cewa takardar ba daga gare ta ta fito ba, kuma babu wani tsari na fara biyan bashin da NELFUND ko Gwamnatin Tarayya suka fitar.

NELFUND ta jaddada cewa har yanzu ba ta bayar da wata umarni ga ɗalibai da su fara biyan bashin lamunin ba.

Hukumar ta kuma bayyana cewa dokar da ta kafa NELFUND ta tanadi a sarari yadda tsarin biyan bashin yake. A cewar sanarwar, babu wani ɗalibi da ake bukatar ya fara biyan bashi yayin da yake makaranta. Haka kuma, ba a buƙatar biyan bashin idan wanda ya amfana bai samu aikin yi ba bayan ya kammala karatu. Biyan bashin ne kawai zai fara ne bisa tanadin doka, bayan mutum ya samu aikin yi mai albashi.

Hukumar ta ce, tana nan daram kan manufarta ta faɗaɗa damar samun ilimi mai zurfi ta hanyar samar da hanyoyin tallafin kuɗi masu gaskiya da sauƙi ga dalibai.

Ta ƙara da cewa, duk wani sahihin bayani game da lamuni ko tsarin biya zai fito ne kawai ta hanyoyin sadarwa na hukuma na NELFUND da kuma kafafen gwamnatin da aka amince da su.

NELFUND ta yi kira ga ɗalibai, iyaye, makarantu da sauran jama’a da su yi watsi da takardar bogi da sauran rahotannin da ke da alaƙa da ita, tare da guje wa yaɗa bayanan da ba a tabbatar da su ba, waɗanda ka iya haifar da fargaba da ruɗani a tsakanin ɗalibai.

A ƙarshe, hukumar ta gode wa masu ruwa da tsaki bisa haɗin kai da suke ba ta, tare da sake jaddada ƙudurinta na bin doka da oda, gaskiya da kuma kare jin daɗin ɗaliban Nijeriya.

By ukarofi