Kungiyar masu rajin kare haƙƙin ɗan adam mai suna Human Rights Activists News Agency ta fitar da rahoto cewa “jami’an tsaro na Iran sun kashe aƙalla mutane 5,777, ciki har da yara ƙanana 86, yayin da ake ƙoƙarin murƙushe zanga‑zangar lumana da ƙaruwar adawa da gwamnati.” Wannan rahoto ya kuma nuna cewa aƙalla mutane kusan 42,000 an kama su yayin rikicin da ya ɗauki hankali a cikin ‘yan watanni.
Rahoton ya jawo cece‑kuce sosai, inda ƙungiyoyin kare haƙƙin ɗan adam ke bayyana cewa ana amfani da makamai da ƙarfi fiye da kima wajen murƙushe ‘yan adawa, lamarin da ya jawo tir da dama daga kasashen duniya kan yadda ake gudanar da al’amura a ƙasar. Saidai da yawa suna kallon wannan rahoton a matsayin ƙarya ta ‘yan kwangilar Amurka wadda ake zargi da kunna wutar cikin gida a ƙasar ta Iran.
