
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Sanannen Malamin addinin Musulunci a Zariya da ke Jihar Kaduna a arewacin Nijeriya, Sheikh Usman Rigi-Rigi Kusfa ya rasu bayan shafe shekaru 57 a duniya.
Wani babban ɗalibinsa mai suna Nasiruddeen Umar da ake kira da Baharu ya sanar da haka ga manema labarai.
Ya ce, Sheikh Kusfa ya rasu ne a safiyar yau Litinin a wani asibitin kuɗi da ke Kaduna bayan fama da wani rashin lafiya da ya shafe watanni yana jinya a kai.
A cewarsa, malamin ya rasu ya bar mata huɗu da ‘ya’ya 37 da kuma jikoki da dama.
Ya ƙara da cewa, za a gudanar da jana’izar marigayin bayan sallar la’asar a gidansa da ke Kusfa a garin Zariya.
Sheikh Usman ya ƙara shahara ne acikin al’umma bisa salon wa’azinsa da ke ɗauke da nishaɗantarwa musamman ganin yadda hakan ya yi tasiri matuƙa acikin masu amfani da kafafen Soshiyal Mediya, lamarin da ya tara masa yawan mabiya.
