Kano: Gobara ta ƙone shaguna a kasuwar Singer

Spread the love

Daga Bridge A. BABAJI a Abuja

A safiyar yau Litinin ne gobara ta lanƙwame wasu sassan kasuwar Singer da ke Jihar Kano a arewacin Nijeriya.

Rahotanni sun bayyana cewa al’amarin ya fara ne tun da asubahin ranar, lamarin da ya kai ga ɓarnata shaguna da rumfuna a wani sashenta.

Da yake tabbatar da faruwar al’amarin, Kakakin Hukumar kashe gobara ta jihar, Saminu Yusuf, ya ce sun samu kiran bada agajin gaggawa da misali ƙarfe 3:16 na dare, wanda ya sa suka gaggauta tura jami’an kashe gobara domin shawo kan al’amarin.

Ya bayyana cewa, har zuwa ƙarfe 10 na safe wani sahse na kasuwar na cigaba da ci da wuta duk da cewa jami’an suna ƙoƙarin daƙile hakan.

Ya ƙara da cewa, za a fitar wasu karin bayanai ga ‘yan daga bisani yayin da ake ƙoƙarin gano musabbabin faruwar iftila’in.

By Babaji