(ci gaba daga makon jiya)
Daga AISHA ASAS
TAMBAYA: Assalamu alaikum. Malama Aisah da farko ina neman ahuwa kan aiko da sako ta murya ba ta rubutu ba. Ni dai matsalata guda zuwa biyu. Matata tana aiki don malamar makaranta ce. To matsalar dai ita ce, ko dannan zuwa can ba ta so ta yi mani nasiha akan sha’anin gida. Bansan ranar da ta siye ko sabulu a gidan ba da niyyar rage min ɗawainiya. Kuma ko Naira biyar na ara to hankali bayya kwanciya sai na biya ta ita. Ko yaranta ma ba abinda take iya yi masu cikin albashinta.
Kwanaki ma wasu kuɗi gwamnati ta ba su ko rance ne ko kyauta ban sani ba, amma a ranar ma magin da za a sa a miya sai da aka yi jira na na dawo daga gareji inda nake aikin gyaran mashi sannan na bayar kafin a dafa miyar.
Shawarar da nake nema ita ce guda biyu. Ta farko zan so ki ja kunnen mata da ke irin wannan hali na matse wa mazajensu nasu aljihu da rashin taimakonsu. Na biyu kuma ina neman shawarar yadda zan yi, don gaskiya ba zan iya barin ta ta ci gaba da yin aikin ba alhali ba na amfana da komai ciki, don ai ni karan kaina na mata ƙoƙari da nake haƙura da wasu buƙatu don na san ta tafi aiki, amma kuma a ce duk abinda ta samo daga ita sai ita.
Abu na farko na san idan na hana ta aikin za mu samu babbar matsala, kuma danginta za su yi ca kaina don su suka tsaya dole sai ta yi aikin.
Ki ba ni shawarar mafita don Allah. Na gode ƙwarai, Allah Ya saka da alheri. Ni ne…………..daga nan………..na gode, na gode. Ma’asalam.
AMSA: Idan ki ka samu damar ɗauke wata hidima ta gida ki yi, hakan na nufin kin yi godiya ne ga Allah da ya ba ki wannan damar, bai bar hannunki a ƙasa a kullum sai kin nemi miji sannan za ki iya yin komai. Ba ke ki ka ba kanki ba, don haka ba yana nufin idan kin yi za su ƙare ba. Wanda ya ba ki, shi ke da ikon amsa ko ƙari gare ki. Hidimar gida ba ta taɓa hana arziki ba, sai ma ta ƙara albarka.
Na san akwai maza maƙetata da suke fatan ganin matansu a ƙasa a kullum, don haka idan sun hango ɗan matsƙi hannunsu, hankalinsu ba ya kwanciya har sai sun lashe shi. Idan kuwa irin wannan miji ki ke da shi, ba laifi idan kin saka ‘yan dabaru na mata, wurin ɓoye sirrinki da yin abinda bai fi ƙarfinki ba.
Shawarar da zan ba ka, idan zai yiwu kada ka hana matarka aikin da take yi, domin duk yadda ka ke ganin ba ta taimaka ma tana yi, domin kula da kanta kawai da take yi taimakon ka ne, kuma sai ta daina ne za ka gano hakan, dalilin da ya sa ba zaka gane ba a yanzu saboda hankalinka ya tsaya a iya cefane ne.
Kuma idan kuna da ‘ya’ya, tanan ma zata taimake ka, domin uwa na da sha’awar ganin ɗanta ya samu ababen more rayuwa, don haka idan tana da za ta yi masu hidima, wadda idan ka yi kaɗan zata iya wadatarwa.
Sai abu na biyu, idan ka hana ta aikin zai iya zama wani tashin hankali tsakaninku, wanda zai iya zama matsala ga kwanciyar hankalin gidan aurenku, ko ku samu babbar matsala da danginta kamar yadda ka faɗa cewa suna sa ido sosai kan sha’anin aikin nata. Wanda hakan kawai zai iya zama barazana ga auren.
Daga ƙarshe, kafin ka yanke hukuncin irin hidimar da ka ke son matarka ta yi maka, ka duba yanayin albashin inda take aiki, domin ba lallai ba ne tana da abinda zata iya yin yadda ka ke so.
Akwai wasu ababe da ke cinye albashin mata lokuta da dama, kasantuwar suna haɗuwa da mutane da dama, ko ince mata ‘yan uwansu, suna ganin yadda suke cin ado da irin kayan da suke sakawa. Idan ba a yi sa’a ba wata mace sai ta yi ta zubar da kuɗin wurin siyan kayan ado don kawai ta cimma wance.
Ko baya ga haka, sanin kowa ne kaso mafi rinjaye na mata ‘yan ƙwalisa ne, halittar mace da ado aka santa, don haka mace ko bata aiki burinta ta tara kayan ado, ta yadda ba za a yi gulmarta kan zanenta kaza ko ta maimaita kaya a bukukunwan da ke kusa.
Sau tari wannan hali ya kai mata da yawa a halaka, a ƙoƙarin samun abin ƙawa wata ta kasa gode wa ƙoƙarin mijinta har ya zama babban ƙalubale a zamantakewar aurensu. Wata kuwa ta biye wa zuciya ta nema a wasu mazan na waje, inda za a yi ban gishiri in ba ki manda, daga nan kuwa sai kawo shegun ɗaka, ko idan mijin ya gano da wuri ya bata jan kati.
Raunin mace yawa ne da shi don haka a duk lokacin da ka biye mata sai a samu matsala, don haka ne ma aka ɗora ragamar kula da ita kanka don ka saisaita ta tare da zame mata ɗan jagora, tamkar raƙumi da akala.
