Har yanzu ba a kammala aiki akan ƙudirin dokar zaɓe ba duk da zaman sirrin Majalisar Dattawa

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Majalisar Dattawa har yanzu ba ta cimma matsaya ba akan ƙudirin gyara wasu sassa na Dokar Zaɓe ta 2022 da aka gano suna da matsala, bayan da ta kasa yanke hukunci a zaman da ta yi na ranar Talata a zaurenta.

Rahotanni sun bayyana cewa, majalisar ta shafe sama da sa’o’i huɗu tana tattauna rahoton wani kwamitin wucin-gadi na mambobi bakwai, wanda aka kafa domin tattarawa da daidaita ra’ayoyi da shawarwarin sanatoci kan ƙudirin dokar.

Tun da farko, majalisar ta fara duba rahoton kwamitin a zaman ta na yau da kullum, kafin daga bisani ta koma zaman musamman domin nazarin takardun da suka shafi ƙudirin gyaran dokar.

Sai dai bayan kammala tattaunawar, Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, bai bayyana sakamakon abin da aka tattauna ba, inda ya ɗage zaman majalisar zuwa ranar aiki ta gaba.

A makon da ya gabata ne majalisar ta kafa kwamitin mambobi bakwai, tare da umarnin su tattara, tace da kuma daidaita dukkan ra’ayoyi da shawarwarin sanatoci kan ƙudirin gyaran dokar zaɓe ta 2022, sannan su gabatar da rahotonsu a ranar Talata.

Sannan, matakin kafa kwamitin ya biyo bayan da majalisar ta shafe sama da sa’o’i biyu tana duba tanade-tanaden ƙudirin dokar a wani zaman na musamman domin ganin ta samar da mafita akan wuraren da ke da matsala.

By Babaji