
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ƙudirin Gyaran Dokar Zaɓe ta 2022 ya tsallake karatu na uku a Majalisar Dattawa.
Haka kuma majalisar ta ƙi amincewa da buƙatar sashe na 60 na ƙaramin sakin layi na uku, wanda ke neman a wajabta miƙa sakamakon zaɓe ta na’ura.
Sashen, wanda majalisar ta yi watsi da shi, da zai buƙaci jami’an Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) su riƙa aike da sakamakon zaɓe ta shafin IREV daga kowace rumfar zaɓe bayan shugaban kula da zaɓen yankin tare da wakilan jam’iyyu sun sanya hannu a sakamakon.
A madadin haka, majalisar dattawan ta amince da dokar da ake amfani da ita, wadda ta ba babban jami’in zaɓe na yanki damar miƙa sakamako ciki har da ainihin adadin masu zaɓen da aka tantance da sakamakon ƙuri’un da aka kaɗa ta hanyar da INEC ta shar’anta.
Da yake jawabi akan al’amarin, Shugaban majalisar, Godswill Akpabio, ya musanta matakin watsi da miƙa sakamakon ta na’ura daga majalisar.
A cewarsa, “tun da ma can miƙa sakamako ta na’ura shi ne dokarmu. Abin da muka yi shine sake jaddada dokar da ake da ita, wadda ta riga ta bada damar miƙawa ta na’ura.
Ya ƙara da cewa, babu wani yunƙuri na yin jinkiri wajen kammala aiki akan ƙudirin dokar zaɓen, kamar yadda aka zarge su sa yi a baya daga ɓangaren adawa.
Kazalika, majalisar ta ƙi amincewa da zaman kurkuku na shekara 10 ga masu saye da sayar da katin zaɓe a ƙarƙashin layi na 22. A madadin haka, za a cigaba da amfani da dokar yin shekara biyu a gidan yari da ƙara tara daga miliyan N2 zuwa N5m.
Har ila yau, ‘yan majalisar sun yi kwaskwarima ga layi na 28 da ya bada damar sanar da zaɓe daga kwanaki 360, wanda aka rage zuwa kwana 180.
