Jami’in shige da fice ya bindige ɗan Nijar a iyakar Katsina

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Wani ɗan Nijar ya rasu bayan zargin wani jami’in Hukumar Shige da Fice (NIS) da harbe shi a mashigar da ke iyakar Burdugu a Ƙaramar Hukumar Ɓauren Jihar Katsina.

Al’amarin ya faru ne da misalin ƙarfe 11:00 na safe a Talata, a lokacin da Sufeto Tijjani Mai Ƙaho, ya yi yunƙurin tsayar da wani akan babur mai kimanin shekaru 30 da ya taho daga Ƙauyen Bace Bace da ke Jamhuriyar Nijar domin duba takardun shige da fice na yau da kullum.

An ce mai babur ɗin, wato Dari Bace Bace bai tsaya ba, lamarin da ya sa jami’in ya harba bindiga, inda alburusai suka ji masa mummunan raunuka a kansa.

Tuni aka garzaya da wanda aka harba zuwa Babban Asibitin Ɓaure, daga bisani aka tura shi Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) da ke Daura, inda ya rasu daga bisani.

Rundunar ‘yan sandan Jihar Katsina ta fara gudanar da bincike akan al’amarin, tana mai cewa an kulle wurin da abin ya faru tare da adana dukkan shaidun da suka dace.

Rundunar ta ƙara da cewa ana cigaba da neman jami’in da ake zargi da hannu a al’amarin domin gudanar da bincike akansa.

By Babaji