Gidauniyar Kannywood ta taya Aina’u Ade murnar zama maitaimakiya ga Gwamnan Kano

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gidauniyar Kannywood (Kannywood Foundation) ta taya fitacciyar jarumar Masana’antar Kannywood Aina’u Ade bisa naɗin da Gwamna Abba Kabir Yusuf ya yi mata na Mai taimaka masa na Musamman akan Al’amuran Kannywood.

Kannywood Foundation ta bayyana naɗin a matsayin ɗora ƙwarya a gurbinta musamman idan an yi la’akari da tsawon shekaru da ta shafe a masana’antar, wanda ya taimaka mata wajen samun ƙwarewa sakamakon jajircewarta, lamarin da ya ta zama ɗaya daga cikin waɗanda suka kawo gagarumin ci-gaba a harkokin Kannywood.

A sanarwar da ta fitar ta hannun Kakakinta, Yakubu Liman a ranar Laraba, gidauniyar ta ce, an yi naɗin a lokacin da ya dace musamman ganin yadda mata suke da muhimmanci a shugabanci da hidimar al’umma.

Kazalika, gidauniyar ta ce tana da yaƙini akan daɗaɗɗiyar jarumar wajen bada gudumuwa ga ci-gaban Kannywood da ƙarfafa ayyukan haɗin gwiwa tsakanin gwamnati da masu ruwa da tsakin masana’antar.

A ƙarshe, Kannywood Foundation ta yi wa Aina’u Ade fatan alheri da samun wa’adi mai tasiri sosai yayin riƙe sabon muƙamin nata.

By Babaji