‘Yan takarar gwamnan APC a Nasarawa sun amince da Farfesa Haruna a matsayin shugaban su

Spread the love

DAGA JOHN WADA a Keffi

Duka ‘yan takaran kujerar gwamnan jihar Nasarawa a inuwar jam’iyyar APC a zaɓen 2027 da ke tafe daga shiyar Yammacin jihar sun amince da Farfesa Injiniya Muhammad Sani Haruna a matsayin shugaban su.

Shugaban jam’iyyar ta APC na karamar hukumar Keffi, Alhaji Mohammed Bello Soja ne ya sanar da haka a jawabin sa a wajen wani taron ƙaddamar da aikin gina wata babbar katanga irin na zamani da ake kira perimeter fencing a turance a makarantar yara na Abdu-Zanga da ke garin Keffi, wanda Farfesa Haruna ɗin ya ɗauki nauyin gudanarwa.

Yace zaɓin Prof. Haruna don jagorantar duka ‘yan takarar da ke shiyar ya kuma samu amincewar tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr. Abdullahi Adamu a lokacin wani zama na musamman da yayi da duka ‘yan takarar a gidan sa da dake Keffi a kwanakin baya.

Shugaban jam’iyyar APC na ƙaramar hukumar Keffi ya ƙara da cewa duka ‘yan takarar kujerar gwamnan ta Nasarawa a shiyar Yammacin jihar sun yanke shawarar zaɓin Injiniya Muhammad Sani Haruna ne bayan sun yi la’akari da baiwar shugabanci nagari da Allah yayi masa musamman yadda ya tafiyar da al’umma a lokacin da yake riƙe da muƙamin shugaban hukumar fasaha da Injiniya da ayuka na musamman wato Chief Executive Officer of the National Agency for Science and Engineering Infrastructure (NASENI) kenan a turance.

A cewar sa tun bayan zaɓin Farfesa Injiniya Muhammad Sani Haruna ɗin a matsayin, jam’iyyar bata samu wani labarin rashin jituwa da gaba tsakanin ‘yan takaran ba duk da waɗannan banbance-banbancen siyasa tsakanin su sabanin yadda lamarin yake a da inda ya alaƙanta hakan ga halin dattijo irin na Farfesan.

Daga nan sai yayi kira ga duka sauran ‘yan takaran da masu hannu da shuni su yi koyi da Farfesa Injiniya Muhammad Sani Haruna a fannin agaza wa al’umma baki ɗaya musamman ta inganta ilimin addini da na zamani.

A nasa ɓangaren tsohon shugaban jam’iyyar APC na ƙasa Dr. Abdullahi Adamu wanda ya samu wakilcin mamba mai wakiltar mazaɓar Nasarawa da Toto a majalisar wakilai ta tarayya Hon. Abdulmumin Ari ya buƙaci mahukuntan makarantar da al’umma baki ɗaya su tabbatar sun kula da ginin katangar bayan an kammala don a dade ana cin moriyar sa inda shima ya buƙaci kowa yayi koyi da Farfesa Haruna.

Itama anata jawabin, sakatariyar ilimi na karamar hukumar Keffi, hajiya Fatima ta gode wa Prof. Haruna game da ba da fifiko ga fannin ilimi inda itama tace dole ne kowa musamman shugabanni suyi koyi da shi.

Tunfarko a jawabin sa, qan takaran gwamnan jihar a APC, Engr. Prof. Muhammad Sani Haruna wato tsohon hukumar ta NASENI) yayi kira ga shugabanni a duka matakai da wadanda Allah ya hore musu arziki su rika tallafa wa kokarin gwamnati ta bai da nasu taimako wa ayukan cigaba wa al’umma musamman a fannin ilimi.

Yace aikin katange makarantar ta Abdu-Zangan daya ne daga cikin dinbin gudumawa da yake bayar wa ilimi kasancewar ilimi shine ginshikin zaman duniya.

Farfesa Injiniya Muhammad Sani Haruna ya kara da cewa aikin kewaye ginin makarantar da yake yi, yana yi ne da nufin hana mallakar filayen makarantar daga waje inda yace bai dace ayi wasi da babban makarantar mai dinbin tarihi ba.

Akarshe sai Farfesa Haruna yayi amfani da damar inda ya bukaci ‘yan siyasa baki daya a jihar suyi koyi da gwamna Abdullahi Sule ta fannin gudanar da ayukan cigaba wa jama’a akoyaushe.

Abubuwa da aka gudanar ayayin taron sun hada da karrama wasu ‘yan jarida da suka taka rawar gani ta yadda labarun gwamnatin jihar da kaddamar da fara aikin ginin katangar a hukumance wadda Farfesan yayi da bai da tallafin zanuwa da sauran su daga gun mai dakin qan takaran da sauran su.

By ukarofi