Gwamnatin Katsina ta jajanta wa al’ummar garin Doma, tare da alƙawarin ƙara tabbatar da tsaro

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta yi alƙawarin ƙara tsaurara matakan tsaro a garin Doma da ke ƙaramar hukumar Faskari, biyo bayan mummunan harin ’yan bindiga da ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 20 tare da lalata dukiyoyi masu yawa.

Gwamna Malam Dikko Raɗɗa ya isar da wannan sakon ta hannun wata tawaga ta musamman ƙarƙashin jagorancin sakataren gwamnatin jihar, Barista Abdullahi Garba Faskari, yayin ziyarar jajantawa da tawagar ta kai wa al’ummar garin.

Tawagar ta ƙunshi sakataren gwamnatin jihar, sakataren dindindin na ofishin SGS, mataimaki na musamman ga gwamna kan harkokin tsaro, kwamishinan ’yan sanda na Jihar Katsina CP Garba Shehu, kwamandan rundunar sojoji ta Birget ta 17, shugaban rundunar tsaron al’umma (Community Watch Corps), da sauran manyan jami’an tsaro.

Tawagar ta kai ziyara fadar Hakimin Mairua, Sarkin Magaji Rafi, Alhaji Sani Sambo Idris, inda ta gana da ɗan majalisar dokokin jihar mai wakiltar Faskari, Hon. Sama’ila Mu’azu Bawa; ɗan majalisar tarayya mai wakiltar yankin, Hon. Shehu Dalhatu Tafoki; shugaban ƙaramar hukumar Faskari, Hon. Sirajo Aliyu Daudawa; da sauran manyan al’umma.

Da yake jawabi a madadin gwamnan jihar, Abdullahi Garba Faskari ya miƙa saƙon ta’aziyya da jajantawa ga iyalan waɗanda abin ya shafa, yana mai bayyana harin a matsayin abin tausayi da raɗaɗi.

“Mutuwa dole ce, amma irin wannan mutuwa abin takaici ne matuƙa. Kowace mutuwa sabuwa ce ga iyalai. Abin da ya dace yanzu shi ne mu yi addu’ar Allah ya amshi shahadarsu, ya gafarta musu,” in ji shi.

Ya bayyana cewa gwamnan jihar ya amince da bayar da tallafin gaggawa na Naira dubu ɗari biyar (₦500,000) ga kowane iyali da abin ya shafa, yana mai cewa duk da cewa babu abin da zai mayar da rai, tallafin na da nufin rage raɗaɗin halin da iyalan ke ciki.

Kwamishinan ’yan sanda na Jihar Katsina, CP Garba Shehu, ya yi magana a madadin sauran hukumomin tsaro, inda ya jajanta wa al’ummar garin tare da tabbatar musu da ƙara ƙaimi wajen kare rayuka da dukiyoyinsu, ba a Doma kaɗai ba har ma a fadin jihar Katsina baki ɗaya.

Da yake mayar da martani a madadin al’ummar Doma, Malam Umar Haruna ya yi Allah-wadai da harin, yana mai bayyana shi a matsayin mummunan ta’asa da rashin imani. Ya ce maharan sun yi barazanar cewa harin da suka kai tamkar gargadi ne na abin da zai biyo baya, tare da roƙon gwamnati da ta dauki matakan gaggawa domin kare rayukan al’umma.

Mutane fiye da 20 ‘yan bindigan suka kashe a garin duk da sasanci ka ƙaramar hukumar Faskari ta yi da ‘yan bindigan.

By ukarofi