Abokan hamayyarmu sun fi mu kashe kuɗi wajen sayen ’yan wasa – Guardiola

Spread the love

Kocin Manchester City, Pep Guardiola, ya yi barkwanci yana mai cewa yana ɗan jin haushin ƙungiyarsa, saboda abokan hamayyarsu sun fi su kashe maƙudan kuɗi wajen cefane.

Man City ce ta fi kashe kuɗi a kasuwar saye da sayar da ’yan ƙwallo da ta ci ta watse a watan Janairu, inda ta sayi Antoine Semenyo daga Bournemouth da Marc Guehi daga Crystal Palace kan kusan fam miliyan 84 gabaki ɗayansu.

Sai dai Guardiola ya ce abokan hamayyarsa a gasar Premier League sun fi zuba jari mafi yawa.

Idan har za a yi ƙididdigar cefane, Man City ta kashe sama da fam miliyan 396 a kaka biyar baya.

Manchester United ce kan gaba da ta kashe fam miliyan 675 sai Arsenal mai fam miliyan 663 da Chelsea mai fam miliyan 651.

Tottenham kuwa ta kashe fam miliyan 574 da Newcastle United mai fam miliyan 424 da kuma Liverpool da ta kashe fam miliyan 420, inji wani bincike.

By ukarofi