Nijeriya na tunkarar kai wa mai tattalin arzikin Dala tiriliyan ɗaya – Idris

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMAMD

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na Nijeriya, Mohammed Idris, ya bayyana cewa matakan gyaran tattalin arziki masu ƙarfin gaske da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya fara tun shekarar 2023 sun fara kai Nijeriya kan hanyar ci gaba, duk da ƙalubale da suka taso a farkon aiwatar da su.

Ministan ya bayyana hakan ne yayin da yake gabatar da lakca ta bikin yaye ɗalibai karo na 34 a Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna, Jihar Neja.

Taken lakcar shi ne: “Matasa da Gina ƙasa: Cin Gajiyar Zamanin Sauye-sauyen ƙasa.”

Idris ya ce, sauye-sauyen da ake aiwatarwa tun 2023 na daga cikin mafi girma da aka taɓa yi a tarihin Nijeriya, yana mai jaddada cewa ba kwatsam aka shiga wannan tafiya ba.

Ya lissafa manyan sauye-sauyen da suka haɗa da cire tallafin man fetur, haɗa farashin canjin kuɗaɗen waje wuri guda, da kuma sabuwar dokar haraji da ta fara aiki daga 1 ga Janairu, 2026.

A cewarsa, tun kafin hawansa mulki, Shugaba Tinubu ya sha alwashin sake fasalta tattalin arzikin ƙasa gaba ɗaya domin samar da ɗorewar ci gaba. Ya ce sanarwar cire tallafin mai a ranar rantsar da shi ta nuna jarumtaka da jajircewa, duk da adawar da ta biyo baya.

Game da sauye-sauyen kasuwar canjin kuɗi, ministan ya ce gwamnati ta kawo tsari da gaskiya a fannin, lamarin da ya rage damar damfara tare da ƙara daidaito a kasuwa.

Haka kuma ya ce sabbin dokokin haraji huɗu da aka kafa sun zama manyan sauye-sauye mafi tasiri a tarihin harajin Nijeriya, duk da cewa an fuskanci yaɗuwar jita-jita da ruɗani a farko.

Idris ya jaddada cewa manufar gyaran haraji ba wai ƙara wa ’yan ƙasa nauyi ba ne, sai dai samar da tsarin da ya fi sauƙi, adalci da kuma gaskiya, tare da bai wa gwamnatocin tarayya, jihohi da ƙananan hukumomi damar samun ƙarin kuɗaɗe domin ayyukan raya ƙasa.

Ya kuma ce sauye-sauyen sun jawo hankalin masu zuba jari na cikin gida da na waje, inda ya ce a fannoni kamar fasahar zamani, noma, tattalin arzikin fasaha da makamashi, ana ganin sabbin damarmaki na bunƙasa.

Dangane da fannin kuɗaɗen waje, ministan ya ce ƙoƙarin da gwamnati ta yi na fitar da Nijeriya daga jerin ƙasashen da ake sa ido a kansu na ƙungiyar FATF a 2025 ya nuna wa duniya cewa an kafa sabon tsarin gaskiya da inganci a harkokin kuɗi.

A ɓangaren matasa, Idris ya bayyana cewa shirye-shirye kamar Asusun Lamunin Ilimi na ƙasa (NELFUND) da shirin horas da matasa miliyan uku a fannin fasaha (3MTT) na daga cikin manyan matakan da gwamnati ke ɗauka domin ƙarfafa matasa. Ya ce tun ƙaddamar da NELFUND a 2024, sama da ɗalibai 900,000 sun amfana, inda aka raba fiye da naira biliyan 174 domin kuɗin makaranta da tallafin rayuwa.

Haka kuma ya ambaci Hukumar Ba da Lamuni ta ƙasa da sauran shirye-shiryen horaswa da tallafa wa matasa a fannoni daban-daban, yana mai cewa gwamnatin Tinubu ta himmatu wajen sauya labarin rayuwar matasan Nijeriya.

A wani ɓangare na daban, Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana cewa Nujeriya na kan “tafiyar murmurewa” domin cimma burin zama tattalin arzikin dala tiriliyan ɗaya nan da shekarar 2030. Mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tattalin arziki da haɗa kan jama’a ta fuskar kuɗi, Dakta Nurudeen Zauro, ya ce cimma wannan buri na buƙatar gina amincewa, samar da ingantattun ababen more rayuwa, da kuma manufofin da ke ƙarfafa haɗin gwiwa.

Ya kwatanta sauye-sauyen da ake yi da tiyata da uba ke amincewa a yi wa ɗansa domin ya samu lafiya, yana mai cewa duk da raɗaɗin da ake ji a yanzu, alamun farfaɗowar tattalin arziki na fara bayyana, yayin da masu zuba jari ke ƙara nuna sha’awa ga Nijeriya.

By ukarofi