’Yan kasuwar fetur sun yi gargaɗin yiwuwar tashin farashi zuwa N1,000

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Masu sana’ar sayar da man fetur a faɗin Nijeriya sun bayyana damuwarsu kan sabon ƙarin farashin mai, suna cewa lamarin na matuƙar takura harkokinsu yayin da ƙarfin jari ke raguwa kuma buƙatar man daga masu saye ke ƙara raguwa.

‘Yan kasuwar sun ce ƙarin farashi ya rage musu ikon sake sayo kaya, lamarin da ya sa wasu daga cikinsu ke haɗawa da juna domin tara kuɗin da za su iya sayen sabon man fetur.

A cewarsu, wannan yanayi na nuna yadda kasuwancin ke shiga wani hali na matsin lamba mai tsanani.

Sun kuma bayyana cewa yawan sayen man fetur ya sauka sosai idan aka kwatanta da watan Disamba, wanda galibi ake ɗaukarsa a matsayin lokacin da ake samun yawan ciniki sakamakon bukukuwa, tafiye-tafiye da kuma ƙaruwar harkokin kasuwanci.

Yayin da yake jawabi kan lamarin, Sakataren Yaɗa Labarai na ƙungiyar ’Yan Kaauwar Man Fetur Masu Zaman Kansu ta Nijeriya (IPMAN), Chinedu Ukadike, ya ce kuɗin da ake buƙata domin sayen cikakken tankin mota na man fetur ya tashi matuƙa.

Ya ce, yanzu ana buƙatar kuɗi masu yawa kafin a sayi lita 40,000 zuwa 45,000 na fetur, abin da ke ƙara jefa ‘yan kasuwa cikin wahala. A cewarsa, da dama daga cikinsu sun kusa ƙarewa da jari, kuma samun kuɗin da za su ci gaba da kasuwanci na ƙara zama ƙalubale. Wasu ma sun fara haɗa jari da juna domin kada su rufe gidajen mai gaba ɗaya.

Wani ɗan kasuwar mai, Ibrahim Gambo, shi ma ya tabbatar da cewa yawan amfani da fetur ya ragu yayin da jama’a ke ƙoƙarin daidaita yawan kashe kuɗi sakamakon tashin farashi. Ya ce buƙata ta yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da Disamba, lokacin da ake samun cunkoson saye saboda shagulgula da zirga-zirga.

Wannan damuwa na zuwa ne a daidai lokacin da ake fuskantar ƙarin matsin lamba a kasuwar mai sakamakon farfaɗowar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya, wanda ya kai kusan dala 70 kan kowace ganga. Masana sun danganta hauhawar farashin da rikice-rikicen siyasa da tsaro a duniya, ciki har da barazanar rikicin soja tsakanin Amurka da Iran, takunkumin sayen man Rasha da kuma ci gaba da buƙatar mai daga ƙasar Sin.

Masana makamashi na gargaɗin cewa farashin ɗanyen mai na iya ci gaba da zama sama yayin da kasuwanni ke la’akari da haɗarin rikice-rikicen duniya, duk da hasashen da aka yi a baya na yuwuwar samun wadatar mai a duniya.

Masu kasuwancin man fetur sun yi gargaɗin cewa idan wannan yanayi ya ɗore, farashin man fetur a famfo – ko na waje ko na cikin gida – na iya tunkarar naira 1,000 kan kowace lita nan gaba kaɗan.

A makon da ya gabata ne ma Matatar Dangote ta sanar da ƙarin farashin fetur daga naira 699 zuwa naira 799 kan kowace lita a matakin siyarwa ga dillalai, matakin da ke ƙara nuna yiwuwar ƙarin farashi a kasuwa baki ɗaya.

By ukarofi