Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Jam’iyyar APC mai mulkin Nijeriya ta ɗauki mataki domin magance jita-jitar rikici da sauya sheƙa a cikin ta, bayan sake saka tsohon Shugaban Jam’iyyar na ƙasa, Sanata Abdullahi Adamu, a shirye-shiryen babban taron ƙasa na jam’iyyar da za a yi a shekarar 2026.
Jam’iyyar ta bayyana kwamitin mutum 73 da zai jagoranci shirye-shiryen taron, inda aka saka sunan Adamu a cikin jerin mambobin kwamitin.
Wannan mataki ya jawo hankalin masu bibiyar siyasa, duba da raɗe-raɗin da suka daɗe suna yawo kan makomarsa a siyasa.
Dawowar Adamu na da muhimmanci matuƙa, musamman ganin cewa a shekarar 2023 ya taɓa bayyana cewa zai ja gefe daga harkokin siyasa, yana mai cewa yana da wata “tsantsani” da ke sa shi nesantar ayyukan jam’iyya. A baya-bayan nan kuma, jita-jita sun karaɗe kafafen sada zumunta na cewa tsohon shugaban ya fice daga APC zuwa jam’iyyar ADC.
Sai dai saka sunansa a matsayin mamba na 32 a cikin kwamitin shirya taron ya nuna a fili cewa har yanzu yana cikin jam’iyyar APC, matakin da ake kallonsa a matsayin ƙoƙarin daƙile waɗancan zarge-zarge.
A watan da ya gabata ma, APC a Jihar Nasarawa, inda Adamu yake da tushe a siyasa, ta fitar da sanarwa tana karyata raɗe-raɗin sauya sheƙar. Jam’iyyar ta ce hoton da ake yaɗawa wanda ake iƙirarin ya nuna shi a wani taron ADC, a zahiri an ɗauke shi ne yayin rajistar mambobin APC ta yanar gizo a faɗin ƙasa.
Kwamitin tsakiya na shirya taron zai kasance ƙarƙashin jagorancin Gwamnan Jihar Imo kuma Shugaban ƙungiyar Gwamnonin APC, Hope Uzodimma. Gwamnan Jihar Kwara, AbdulRahman AbdulRazaƙ, zai kasance mataimakinsa, yayin da Gwamnan Jihar Yobe, Mai Mala Buni, zai riƙe muƙamin sakatare.
Tsarin kwamitin ya nuna yadda gwamnonin APC ke kara samun ƙarfi wajen tafiyar da manyan al’amuran jam’iyyar, musamman a gabanin babban taron ƙasa da ake sa ran zai tsara makomar shugabancin jam’iyyar kafin babban zaɓen shekarar 2027.
Baya ga batun Abdullahi Adamu, jerin sunayen kwamitin ya kuma nuna dabarar da wasu ‘yan cikin jam’iyyar ke kira “babban tanti”, wato haɗin kan tsofaffin jiga-jigan jam’iyya da kuma sabbin masu shiga masu tasiri.
Daga cikin fitattun sunayen da ke cikin kwamitin akwai Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, da Kakakin Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas, tare da wasu gwamnonin jihohi da suka sauya sheƙa zuwa APC a ‘yan watannin nan.
Cikin sabbin waɗanda suka shiga jam’iyyar kuma aka sanya a jerin kwamitin akwai Gwamnan Jihar Rivers, Siminalayi Fubara, Gwamnan Jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, da Gwamnan Jihar Filato, Caleb Mutfwang, wadanda rahotanni suka nuna sun shiga APC a baya-bayan nan.
