
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Jam’iyyar APC ta maye gurbin Gwamna Hope Uzodimma na Jihar Imo da tsohon Gwamnan Jihar Katsina, Aminu Bello Masari a muƙamin shugaban kwamitin shirya babban taronta na ƙasa, wanda za a yi a ranakun 27 da 28 ga watan Maris, 2026.
Da yake bayyana haka ta kafar X a ranar Juma’a, Sakataren yaɗa labaran APC na ƙasa, Surajudeen Basiru ya ce Uzodimma, wanda da fari aka naɗa shi jagoran kwamitin, zai riƙe muƙamin ma’aji.
Haka kuma jam’iyyar mai mulki ta faɗaɗa adadin mambobin kwamitin daga 73 zuwa 90 a wani yunƙuri na shigar da ƙarin masu ruwa da tsaki cikin al’amarin.
Basirun ya kuma bayyana cewa an sake tsarin kwamitin ne bayan gudanar da ƙarin shawarwari daga shugabancin jam’iyyar da masu ruwa da tsaki a mataki na ƙasa.
Ya ƙara da cewa, za a sanar da ƙananun kwamitocin da ke ƙarƙashin babban kwamitin da aka samar a lokacin da ya dace.
