Daga DAUDA USMAN
Wani matashi kuma ɗan kasuwa a Kano, Alhaji Salisu Haruna, mazaunin garin Jajirawa da ke ƙaramar Hukumar Kiru a Jihar Kano, ya jagoranci gudanar da taron addu’o’i na musamman domin neman ƙarin zaman lafiya a jihar Kano da kuma ƙasa baki ɗaya.
Taron ya samu halartar malamai, magabata, da ɗumbin al’ummar garin Jajirawa da Kiru, har ma da wasu daga sassan jihar Kano.
An gudanar da taron ne a harabar Masallacin Juma’a na garin Jajirawa a ranar Asabar da ta gabata.
Daga cikin iyayen taron akwai Mai Martaba Dagacin garin Bargone, Alhaji Abdullahi Muhammad, da Mai Unguwar Jajirawa, Dauda Haruna Kiru, tare da sauran masu ruwa da tsaki a yankin.
Tun bayan buɗe taron da addu’a, malamai da dama sun gabatar da wa’azi ga al’ummar Musulmi kan muhimmancin zaman lafiya, tare da ƙarfafa musu gwiwa kan bin tafarkin tsoron Allah a harkokin rayuwarsu na yau da kullum. Sauran malaman kuma sun ci gaba da gudanar da addu’o’i na musamman, suna rokon Allah Ya cigaba da zaunar da Kano lafiya, da Arewa baki ɗaya, har ma da ƙasa gaba ɗaya.
A yayin taron, Babban Limamin Masallacin Juma’a na ƙaraye, Malam Usman, ya jagoranci sauran malamai wajen gudanar da addu’a a bainar jama’a. Haka kuma, an ɗaura auren Maharazu Sani da amaryarsa Malama Na’ima Muwadda Jajirawa, inda aka yi musu fatan zaman lafiya da albarka.
Mahaifin ango, Alhaji Sani Jajirawa, ya gabatar da jawabin godiya ga ɗimbin al’ummar da suka halarci taron, tare da yi musu fatan alheri yayin komawarsu gidajensu lafiya.
Shi ma a nasa ɓangaren, jagoran taron addu’ar, Alhaji Salisu Haruna Jajirawa, ya nuna farin cikinsa bisa yadda al’umma suka ba da haɗin kai da goyon baya wajen amsa kiran taron. Ya ce babu abin da zai ce face godiya ga Allah da kuma duk wanda ya samu halarta. Haka kuma ya yi wa kowa fatan komawa gida lafiya.
A ƙarshe, ya ja hankalin matasa da su tashi tsaye wajen neman ilimi tare da koyon sana’o’in hannu domin dogaro da kai da kuma kyautata makomar rayuwarsu.
