Sai an inganta rayuwar matasa ƙasa za ta bunƙasa – Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban Nijeriya Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa babu wata ƙasa da za ta iya samun ci gaba mai ɗorewa idan ba ta zuba jari kai tsaye a rayuwar matasanta ba, musamman ta fuskar ilimi da bunƙasa ƙwarewa.

Shugaban ya bayyana hakan ne ta bakin ƙaramar Ministar Ilimi, Farfesa Suwaiba Sa’id-Ahmad, wadda ta wakilce shi a bikin yaye ɗalibai karo na 34 da kuma cikar jami’ar shekaru 43 da kafuwa na Jami’ar Fasaha ta Tarayya da ke Minna (FUT Minna).

A cewar shugaban, bai kamata wani ɗan Nijeriya ya rasa damar samun ingantaccen ilimi ba saboda tangarɗar kuɗi.

Ya jaddada cewa gwamnatinsa na ɗaukar matakai na faɗaɗa damar shiga makarantu ta hanyar zuba jari a gine-gine da kayayyakin more rayuwa, tare da aiwatar da tsarin rancen ɗalibai domin sauƙaƙa musu nauyin kuɗin karatu.

Tinubu ya yaba da irin gagarumin rawar da FUT Minna ta taka tsawon shekaru 43 da suka gabata, inda ya ce jami’ar ta zama cibiyar ƙwarewa a fannin kimiyya, injiniyanci, ƙirƙire-ƙirƙire da bincike mai amfani ga al’umma.

Shi ma a nasa jawabin, Mataimakin Shugaban Jami’ar, Farfesa Farouk Kuta, ya ce bikin ya zama wata shaida ta jajircewa, ƙirƙira da kuma sadaukarwar al’ummar jami’ar wajen bunƙasa ilimi da hidimtawa bil’adama.

Ya bayyana cewa shekarar da ta gabata ta zo da manyan nasarori, inda jami’ar ta zama ta bakwai mafi kyau a Nijeriya, kuma ta fi kowace jami’a mai fanni na musamman matsayi a ƙasar.

Haka kuma ya ce jami’ar na cikin manyan jami’o’i goma mafi daraja a Nijeriya, sannan ta kasance ta 68 a nahiyar Afirka.

Ya ƙara da cewa, faɗaɗa jami’ar da ake yi wani muhimmin mataki ne na cika burinta na zama jami’a mai dogaro da fasaha wadda ke magance matsalolin al’umma, musamman a fannin horas da ma’aikatan jinya da masu fasahar kiwon lafiya.

Farfesa Kuta ya kuma bayyana cewa jami’ar na bai wa ma’aikata muhimmanci, inda aka ƙara wa manyan ma’aikata marasa koyarwa 146 girma, tare da ƙara wa ƙananan ma’aikata 110 matsayi. Haka zalika, an tabbatar da naɗewar ma’aikata 22 a hukumance.

Ya ƙara da cewa, an gyara asibitin jami’a da kuma filin wasanni domin samar da yanayi mai kyau ga ɗalibai da ma’aikata.

Shugaban Majalisar Gudanarwar Jami’ar, Dakta Mohammed Santuraki, ya yaba wa Shugaba Tinubu kan sauye-sauyen da gwamnatinsa ke yi domin bunkasa ƙasa. Haka kuma ya gode wa Gwamnan Jihar Neja, Umaru Bago, bisa tallafin naira miliyan 100 da ya bayar domin gina ɗakunan kwanan ɗalibai mata na fannin likitanci.

ɗaya daga cikin fitattun ɗaliban da suka kammala karatu, Koter Oluwadamilola daga Sashen Injiniyan Lantarki da Na’urorin Wutar Lantarki, ta ce nasarar da suka samu shaida ce ta haƙuri da haɗin kai da ya taimaka musu tsawon lokacin karatunsu.

Jimillar ɗalibai 5,297 ne jami’ar ta yaye a zangon karatu na shekarar 2024/2025.

By ukarofi