’Yan kasuwar Onitsha sun buɗe shaguna bayan umarnin gwamna Soludo

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

’Yan kasuwar babbar kasuwar Onitsha a jihar Anambra sun koma bakin aiki tare da buɗe shagunan su, bayan bin umarnin da Gwamna Chukwuma Soludo ya bayar na dakatar da biyayya ga dokar zaman gida da wasu ƙungiyoyi ke ƙaƙaba wa a yankin Kudu maso Gabas.

Rahotanni sun nuna cewa mako guda bayan gwamnatin jihar ta rufe kasuwar domin ladabtar da masu ƙin bin umarni, ’yan kasuwar sun fara komawa tun da sassafe domin ci gaba da harkokin su na yau da kullum.

Tun misalin ƙarfe 8:45 na safiyar ranar Litinin, an fara ganin masu saye da sayarwa suna cika manyan hanyoyin shiga kasuwar.

Daga yankin Egerton zuwa kasuwar kayan abinci ta Ose, har zuwa Young Park da ke ɗaya daga cikin manyan ƙofar shiga kasuwar, shaguna da dama sun buɗe yayin da kwastomomi ke fara tururuwa domin saye.

Haka zalika, daga Emeka Offor Plaza zuwa titin Sokoto, Lagos Line da Marine, harkokin kasuwanci sun fara dawowa yadda aka saba.

Tun a makon da ya gabata ne Gwamna Soludo ya bayar da umarnin rufe kasuwar na tsawon mako guda, bayan da aka zargi ’yan kasuwa da bin dokar zaman gida ta ranar Litinin wadda gwamnatin jihar ta bayyana a matsayin barazana ga tattalin arziki da zaman lafiya. Gwamnan ya gargaɗi ’yan kasuwar cewa duk wanda bai buɗe shago ba bayan wa’adin, za a ƙƙra tsawaita rufe kasuwar.

Gwamnatin jihar ta sha nanata cewa dokar zaman gida da wasu ƙungiyoyi ke ƙaƙabawa ba ta da tushe a doka, kuma tana jawo babbar asara ga tattalin arzikin yankin. Ta buƙaci mazauna jihar su riƙa gudanar da harkokin su ba tare da fargaba ba, tana mai jaddada cewa an ɗauki matakan tsaro domin kare rayuka da dukiyoyi.

A yayin da ’yan kasuwar ke komawa bakin aiki, jami’an tsaro ciki har da ’yan sanda da sojoji sun baza a wurare daban-daban domin tabbatar da zaman lafiya da kuma hana duk wani yunƙuri na tilasta rufe kasuwanni.

Shekaru da dama kenan ana fama da matsalar zaman gida a sassan yankin Kudu maso Gabas, lamarin da ya shafi kasuwanni, makarantu da ofisoshi, musamman a biranen kasuwanci kamar Onitsha. Duk da cewa gwamnatin Anambra ta sanar tun a 2022 cewa an kawo ƙarshen lamarin tare da shirye-shiryen sulhu da yafiya ga matasa, har yanzu wasu na ci gaba da zama a gida saboda tsoro.

Komawar ’yan kasuwar Onitsha bakin aiki na nuni da ƙaruwar amincewa da ƙoƙarin gwamnatin jihar na dawo da cikakken zaman lafiya da farfaɗo da tattalin arziki a yankin.

By ukarofi