Yadda gobara ta laƙume dukiyar miliyoyin Naira a kasuwar Singer ta Kano

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Wata gobara da ta tashi da sanyin safiyar Litinin ta yi ɓarna a wasu sassa na babbar kasuwar Singer da ke birnin Jihar Kano, lamarin da ya jawo fargaba a tsakanin ’yan kasuwa da mazauna yankin.

Rahotanni sun nuna cewa wutar ta kama ne da misalin ƙarfe uku da mintuna sha shida na asuba, inda ta fara ƙonewa a wasu shaguna kafin ta bazu zuwa wasu wurare na kasuwar mai cike da cunkoso da harkokin kasuwanci.

Mai magana da yawun Hukumar Kashe Gobara ta Jihar Kano, Saminu Yusif, ya tabbatar da faruwar lamarin, yana mai cewa sun samu kiran gaggawa kuma nan take suka tura jami’ansu domin daƙile yaɗuwar wutar.

A cewarsa, har zuwa misalin ƙarfe goma na safe, an ci gaba da ƙoƙarin kashe sauran wutar da ke ci a wasu sassa na kasuwar, yayin da jami’an kashe gobara ke aiki tuƙuru domin hana ta bazuwa zuwa ƙarin shaguna da gine-gine da ke makwabtaka da wurin.

Ya ƙara da cewa, za a fitar da cikakken bayani dangane da musabbabin gobarar da kuma girman ɓarnar da aka yi da zarar an kammala bincike.

Kasuwar Singer na ɗaya daga cikin manyan kasuwanni a Kano da ke ɗauke da shaguna iri-iri, inda dubban ‘yan kasuwa ke gudanar da sana’o’insu a kullum. Gobarar ta haddasa asarar dukiya mai yawa, duk da cewa har yanzu ba a fitar da takamaiman ƙididdigar asarar ba.

A wani lamari makamancin haka a kwanakin baya, gobara ta kuma tashi a wani ginin bene mai hawa biyu a yankin Omagba Phase 2 da ke Onitsha ta Arewa a Jihar Anambra. Wutar ta yi ajalin wata tsohuwa mai shekaru 95 da aka ce ta maƙale a cikin ginin na tsawon lokaci kafin a samu nasarar kashe gobarar.

Rahotanni sun ce wutar ta tashi ne da yammacin Juma’a da misalin ƙarfe biyar da mintuna goma sha biyar, inda ta bazu zuwa wasu ɗakuna kafin jami’an kashe gobara su samu nasarar shawo kanta bayan dogon lokaci tare da taimakon mazauna yankin.

Waɗannan al’amura na sake jaddada muhimmancin ɗaukar matakan kariya daga gobara, musamman a wuraren kasuwanci da gidajen zama masu cunkoso, domin rage asarar rayuka da dukiyoyi.

By ukarofi