Sabbin takardun Epstein da girman abinda yake ƙunshe a ciki

Spread the love

Daga AISHA ASAS

Fitar da sabbin takardu sama da miliyan uku kan shari’ar Jeffrey Epstein ya sake zama batu mafi tattaunawa a kafafen sada zumunta tare da tayar da hankulan al’umma fiye da ƙima, wanda hakan ya sa ya kasance lamarin da ya fi komawane tashe a wannan makon. Haka muka ya zama abu da ya sanya ɗimbin tambayoyi a zukatan dubatan mutane daga koina a faɗin duniya.

Duk da cewa, Ma’aikatar Shari’a ta Amurka ta bayyana wannan bankaɗo takardun da ta yi a matsayin babban mataki na yunƙurin bayyana gaskiya, saidai masana doka da kuma shahararrun ‘yan jaridu da suka san makamar aiki na ganin abinda aka fitar bai watadar ba wurin amsa tambayar da ta fi damun mutane ta, ina gaskiyar take?

A zahiri Epstein ba shi ne babban labarin da ya ja hankalin jama’a ba, babban labarin da ya ja hankullan al’umma shi ne tsarin da ya ba shi kariya tsawon shekaru. Rahotannin manyan jaridun duniya sun nuna cewa, Epstein ya kewaye kansa da fitattun ‘yan siyasa, attajirai da shahararrun mutane, wanda yake shiga cikin rigarsu don samun makafa daga hukunci. Wannan ya amsa tambayar al’umma ta ko iko da kuɗi na iya rufe idon doka? 

Duk da yawan takardun da aka fitar, bincike ya tabbatar da an rufe sunayen mutane da dama da kuma muhimman bayyanai kansu, wanda hakan na nufin ana ba wa wasu kariya. 

Saidai ita gwamnati ta tabbatar da an yi hakan saidai ba da dalilin da mutane ke tunani ba, wato ba wa masu iko kariya, maimakon haka ta bayyana wannan runƙuri a matsayin kare mutuncin waɗanda aka zalunta ta hanyar ɓoye su. Duk da hakan masu sharhi na cewa, hakan bai zama hujja mai ƙwari ba, domin ta yaya za a san cikakkiyar gaskiya idan aka ɓoye wasu sassan labarin. Kuma al’umma na ganin ta hanyar amfani da kare waɗanda aka zalunta ne za a iya shigar da waɗanda ake son ba wa kariya.

A ɓangare guda, a kafafen yaɗa labarai da na sada zumumta ɗinbin mutane sun nuna takaicinsu kan ababen da suka bayyana ciki kuwa har da ganin wasu fuskoki da bai kamata a gani ba sakamakon girmama su da ake yi da kuma yadda lamarin ke tafiya ta fuskar shari’a. 

A ganinsu, fitar da takardun ba tare da gurfanar da waɗanda suka aikata laifin ba tamkar nuna rauni ne ba tare da magani ba. Wannan ya ƙara dasa shakku kan sha’anin shari’a musamman idan ta shafi masu faɗa a ji.

Idan muka yi duba da irin fuskokin da aka bayyana da bayyanan ababen ƙazanta da suka aikata a koina a faɗin duniya, za mu fahimci cewa duniya ta zo matakin da za mu iya cewa mutanen kirki sun zama mafi tsada a cikin ababe masu tsada waɗanda samun su ya fi samun mafi tsada daga albarkatun da ke cikin ƙasa.

Lamarin rashin hukunta masu laifi saboda ikon da suke da shi ya zama ɗaya daga cikin ababen da ke ci wa al’ummar Najeriya tuwo a ƙwarya, saidai wannan lamari na Epstein ya bayyana mana cewa duk kanwar ja ce, bambancin kawai namu babu tsoro bare kunya a ciki. 

By ukarofi