Majalisar Dattawa ta amince da watsa sakamakon zaɓe ta na’ura bayan ƙorafin ‘yan ƙasa

Spread the love

Majalisar Dattawa ta ce ta amince da aika sakamakon zaɓe kai-tsaye ta na’ura a matsayin matakin farko na aika sakamakon, amma idan aka samu matsalar sadarwa, INEC za ta yi amfani da takarda a rubuce wajen aika sakamakon kamar yadda aka saba yi a baya.

Sanata Tahir Munguno ne ya gabatar da ƙudirin a lokacin zaman gaggawa da majalisar ta yi akan dokar, yayin da shugaban majalisar, Godswill Akpabio ya amince da ƙudirin bayan amincewar sauran ‘yan majalisar.

Daga nan ne majalisar ta kafa kwamiti mai mambobi 12 domin yin aiki da Majalisar Wakilai don tsefe dokokin kamar yadda tsarin amincewa da dokoki ya tanada.

Majalisar ta kira zaman gaggawar ne bayan da ƙungiyoyin fararen hula da jam’iyyun adawa suka mamaye harabar majalisar dattawan a ranar Litinin domin gudanar da zanga-zanga don nuna adawarsu ta ƙin amincewa da majalisar ta yi na wajabta aikata sakamakon zaɓe ta na’ura kai-tsaye daga kowace rumfar zaɓe.

Tun da farko Majalisar Wakilai ta amince ta duka ƙudurorin gyaran dokar zaɓen ba tare da ƙebe kowane ba daga cikinsu.

Amma a nata ɓangaren majalisar dattawan ta keɓe sashen da ya yi magana akan wajabta aika sakamakon kowace rumfa kai-tsaye ta na’ura ta yadda kowane ɗan ƙasa zai gan shi daga duk inda yake.

Majalisar ta kafa hujja da rashin ingantaccen sabis ɗin intanet da rashin tsaro a wasu ƙauyukan ƙasar a matsayin dalilansu na rashin wajabta aika sakamakon zaɓen kai-tsaye ta na’ura.

By Babaji