Da Ɗumi-Ɗumi: Tottenham ta sallami koci Thomas Frank

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham Hotspur, ta sallami mai horar da ‘yan wasanta, Thomas Frank bayan shan kaye a hannun Newcastle United da ci 2 da 1 a ranar Talata.

Frank, wanda ya karɓi ragamar jagorancin kulob ɗin a kakar bara bayan barin Brentford, ya bar Spurs a gurbi na 16 a teburin gasar Premier League, kuma maki biyar daga rukunin ƙungiyoyi uku da ke fuskantar barazanar fita a gasar a kaka ta gaba.

Tottenham ta shiga halin tsaka-mai-wuya a 2026 bayan gaza yin nasara a koda wasa ɗaya ne daga cikin takwas da ta buga.

Haka kuma ɗan ƙasar Denmark ɗin ya bar ƙungiyar da kaso mafi rauni na samun nasarori a wasannin gida tun 2008.

Rashin nasarar ta ranar Talatar ta nuna yadda ƙungiyar ke fafutukar samun tsarin wasa mai kyau da ɗorewar tsaron gida.

An naɗa Frank a matsayin kocin Tottenham ne bisa la’akari da yadda ya yi amfani da matsakaitan ‘yan wasan wajen gwabzawa cikin nasara da manyan ƙungiyoyin gasar a zamansa na Brentford.

Kawo yanzu dai ƙungiyar arewacin Landon ɗin ba ta fitar da wani saƙo ba a hukumance game da batun sauyin mai horar da ‘yan wasan nata.

By Babaji