Batun haramta giyar leda na nan daram, inji NAFDAC

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar kula da Ingancin Abinci da Magunguna ta Ƙasa NAFDAC, ta ƙaryata rahotannin da ke zargin cewa Gwamnatin Tarayya ta umarce ta akan ta dakatar da matakin da ta ɗauka na haramta barasar ledar ‘sachet’ da na kwalaben PET masu nauyin 200ml.

A kwanan nan wasu rahotanni suka yi ikirarin cewa Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (OSGF) ya umarci NAFDAC da ta dakatar da matakin nata na dakatarwar.

Hukumar, a wata takarda daga Darakta Janar ɗinta, Mojisola Adeyeye, ta ce wannan saƙon ba gaskiya ba ne, abu ne da aka ƙirƙira da nufin ruɗar da jama’a.

Don haka bai shafi wani saƙo da hukumar ke amsa a hukumance ba daga ofishin gwamnati ba akan al’amarin.

NAFDAC ta kuma ba ta taɓa karɓar wani umarni da ke neman ta soke wani haramci da ta akan wani al’amari ln aikin ba daga gwamnati.

A cewarta, tana aiki tuƙuru wajen cigaba da bada kariya ga lafiyar al’umma da tabbatar da an kiyaye su gami da sauke nauyinta bisa yadda doka ta tsara.

A ƙarshe, ta yi kira ga ɗaukacin al’ummar ƙasa da su riƙa tantance labarai kafin amincewa da su, tana mai cewa ana samun rahotanni matakan da ta ke ɗauka ne ta sahihan kafafen watsa labarai da ta amince da su a hukumance.

By Babaji