Dujiman Katsina ya ƙarɓi baƙuncin jami’an kashe gobara tara da ya sama wa aiki

Spread the love

Hon Abdullahi Aliyu(Dujiman Katsina) shugaban kwamitin cikin gida na majalisar wakilai wanda shine ya samar masu aikin,ya ƙarɓi baƙuncin su ne bayan da suka sami ƙarin girma.

Jami’an sun kawo masa ziyarar ne domin gabatar masa da satifiket wanda aka basu bayan karɓar horo a fannin kashe gobara a garin Jos da ke jihar Filato.

Ɗan majalisar ya taya su murna tare da nanata ƙudirin sa na cigaba da samar da ayyukan yi da sauran kayan more rayuwa ga al’ummar ƙananan hukumomin Musawa da Matazu.

Dujima ya kuma yi alƙawarin cigaba da samarwa matasan yankin da aikin yi da tura su cibiyoyin koyar da sana’o’i da ba su tallafi bayan sun gama samun horo.

Ɗan majalisar wanda ke wakiltar ƙananan hukumomin Musawa da Matazu ya samar wa matasa da dama aiki musamman a ma’aikatar harkokin cikin gida na gwamnatin tarayya.

Hukumomin kuwa sun haɗa da sashin shigi da fice, sibil difens, hukumar kashe gobara da sauran su.

By ukarofi