Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Gwamnan Jihar Katsina, Malam Dikko Raɗɗa ya jagoranci ƙaddamar da rabon kayan abinci da kayan amfani na yau da kullum ga masu buƙata ta musamman su 1,500, tare da mutane 494 da iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa a shekarar 2025, daga ƙananan hukumomi 25 na Jihar Katsina.
A jawabin ta a wajen taron, shugabar hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Katsina (SEMA), Hajiya Binta Hussaini Dangani, ta bayyana cewa wannan shiri na daga cikin manyan ayyukan jin ƙai da gwamnatin jihar Katsina ke aiwatarwa domin tallafa wa al’umma masu rauni inda tace hukumar SEMA ta ɗauki lokaci tana tantancewa da gano masu buƙata ta musamman da kuma waɗanda ambaliyar ruwa ta shafa, domin tabbatar da cewa tallafin ya isa ga waɗanda suka fi buƙatarsa.
Hajiya Binta ta ƙara da cewa rabon kayan abinci da kayan amfanin yau da kullum ba kawai taimako ba ne na gaggawa illa wata hanya ce ta rage raɗaɗin rayuwa da kuma nuna kulawa ta musamman ga waɗanda ke fuskantar ƙalubale iri-iri.
Ta jaddada cewa gwamnatin Jihar Katsina ƙarƙashin jagorancin Malam. Dikko Umar Raɗɗa tana da ƙuduri na musamman na ganin babu wani ɗan jihar da za a bari hakanan musamman masu buƙata ta musamman ta kuma yaba wa gwamnan bisa goyon bayan da yake bai wa hukumar SEMA domin sauke nauyin da aka ɗora mata yadda ya kamata.
Da yake ƙaddamar da rabon Kayan Gwamna Dikko Raɗɗa, ya bayyana jin daɗin sa da ganin wannan shiri ya tabbata, inda ya ce wannan tallafi wani bangare ne na manufofin gwamnatinsa na jin ƙai ga al’umma, gwamnan ya bayyana cewa gwamnati ta fahimci irin wahalhalun da masu buƙata ta musamman da kuma waɗanda iftila’in ambaliyar ruwa ya shafa ke fuskanta, musamman sakamakon matsalolin matsin lamba da tattalin arziki da sauransu.
Malam Dikko Umar Raɗɗa ya jaddada cewa gwamnatinsa za ta ci gaba da ɓullo da irin waɗannan shirye shirye domin rage raɗaɗin da dawo da martabar rayuwa ga waɗanda suka samu kansu cikin mawuyacin hali
Ya kuma yi alƙawarin cewa gwamnati ba za ta tsaya a nan kaɗai ba, domin za a ci gaba da tallafa wa ɓangarori daban-daban na al’umma ta hanyoyin da dama domin samun walwalar rayuwa.
Gwamnan ya yabawa hukumar bada agajin gaggawa ta Jihar Katsina (SEMA) bisa jajircewa da gaskiyar aiki da take nunawa wajen gudanar da ayyukanta, ya ce irin wannan tsari da aka bi wajen rarraba kayayyakin cikin adalci da tsaro abin koyi ne, tare da kira ga waɗanda suka amfana da tallafin da su yi amfani da shi yadda ya dace.
