
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
A wannan shekara ta 2026 ne aka halaka tsohon Shugaban mulkin soji na Nijeriya, wato Murtala Muhammed.
Ɗaya daga cikin waɗanda da suka shaida kisan marigayin kuma yaron aikinsa mai suna Michael Otuwe (mai ritaya) ya bayyana yadda yunƙurin juyin mulkin na 1976 da bai yi nasara ba ya faru.
A wata hira da manema labarai, tsohon jami’in ya bayyana yadda marigayin ya rage saura ƙiris ya tsallake wa maharan nasa, ƙwarewarsa na lokacin yaƙin basasa da shekarun da ya ɗauka waken yi wa Nijeriya hidima, lamarin da ya sa ya zama ɗaya daga cikin jajirtattun ‘yan mazan jiya.
A hirarsa da Daily Trust, Otuwa ya ce, “Ni mutumin ƙabilar Igala ne daga Ƙaramar Hukumar Olamaboro na Jihar Kogi. Na yi Makarantar Firamare ta Ankpa da ‘Ankpa Model Secondary School’ gabanin da shiga aikin (soja) da na fi so.”
A cewarsa, Murtala ya zaɓi yin aiki da shi ne bisa tsaftarsa da ya gani a lokacin da suka haɗu a rukunin horarwa ta ‘Nigerian Army Signal Corps’.
Ya bayyana tsohon mai gidan nasa a matsayin jami’i masanin dabarun aiki da zama kwamandan sojoji ƙwararre, musamman bisa la’akari da rawar da ya taka a yayin yaƙin basasa.
A ranar 13 ga watan Fabarairun 1976, wasu matasan hafsoshin tsaro da suka kira kansu “masu son kawo canji” suka sanar da kifar da gwamnatin Murtala.
Jagoransu, Bukar Suka Dimka wanda a lokacin yake da muƙamin laftanar kanal ne ya harbe Marigayi Murtala Muhammad a lokacin da yake tafiya a cikin mota.
