Zargin badaƙalar N2.4bn: Tsohuwar Minista, Stella Odua na neman sasanci da Antoni Janar na Tarayya

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A ranar Alhamis, wata Babbar Kotu da ke zaune a Maitaman Birnin Tarayya Abuja ta samu bayanin cewa tsohuwar Ministar Sufurin Jiragen Sama, Frinses Stella Adaeze Odua ta fara tattaunawa da Antoni-Janar na Ƙasa (AGF) bisa neman sasanci akan shari’arta ta badaƙalar Naira biliyan 2.4.

An samu wannan ci-gaba ne a lokacin da aka tayar da batun shari’ar a gaban Mai Shari’a Hamza Mu’azu, inda lauyan ɓangaren masu binciken ya bayyana cewa tsohuwar ministar ta nemi a sasancin ne a ƙarƙashin kundin dokar manyan laifuka ta ACJA 2015 da ya ba ta damar hakan.

A ranar 10 ga watan Disambar 2025 ne aka gurfanar da Odua da tsohuwar mataimakiyarta, Gloria Odita a kotu bisa zargin su laifuka biyar masu alaƙa da zargin sauya akalar kuɗaɗe da mallakar dukiyar al’umma ta haramtattun hanyoyi da adadinsu ya kai N2,459,030,733.50.

Tun a ranar 14 ga watan Oktoban 2025 ne aka shigar da ƙarar ta ofishin AGF ɗin.

A yayin shari’ar, Daraktan kula da lamuran shari’ar manyan laifuka na ƙasa (DPPF), Rotimi Oyedepo SAN) ya ce ɓangarensu ya samu takardar buƙatar shirya tattaunawar sasantawa da AGF ɗin daga Odua.

Daga nan ya nemi kotun da ta ɗage sauraron shari’ar din bai wa ɓangarorin biyu damar nazari da aiki akan al’amarin tare da dawowa domin bada ba’asin abin da suka cimma.

Haka ma ɓangaren lauyoyin masu kare waɗanda aka shigar ƙara, Tobechukwu Michael da Wale Balogun, sun tabbatar da matsayin ɗaya ɓangare, sannan ba su nemi ja da buƙatar ɗage shari’ar ba.

Daga nan ne Alƙali Mu’azu ya ɗage zaman zuwa ranar 5 ga watan Maris.

By Babaji