Kotu ta yanke wa jarumar Kannywood, Samha Inuwa hukuncin ɗaurin wata shida kan wulaƙanta takardar Naira

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

A yau Juma’a Mai Shari’a S.M Shu’aibu na Babbar Kotun Tarayya da ke zaune a Kano ya yanke wa jarumar Kannywood, Sa’adatu Mohammed Inuwa da aka fi sani da Samha hukuncin wata shida a gidan yari.

An yanke wa jarumar hukuncin ne bayan samun ta da laifin wulaƙanta takardar Naira, wanda hakan saɓa wa doka ne.

Laifin Samha ya ci karo da dokar Babban Bankin Nijeriya (CBN) na 2007.

A kwanakin baya ne Hukumar Hana yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati EFCC ta gurfanar da Samha bisa tuhumar ta da laifin wulaƙanta Naira.

An ga yadda jarumar take fyace hanci da N1,000 a wani faifan bidiyo duk da cewa ta yi ikirarin hakan abu ne da ya faru a shekarun baya.

By Babaji