‘Yan majalisar Amurka na nazarin haramta wa Kwankwaso da Miyetti Allah biza kan zargin tauye ‘yancin addini

Spread the love

‘Yan majalisar wakilan Amurka sun gabatar da wani ƙuduri a zauren majalisar wanda ya ƙunshi rahoto kan kwamitin bincike game da zargin cin zarafin Kiristoci da musguna musu a Nijeriya.

Haka nan rahoton ya bayar da shawarwari kan matakan da suka dace Amurka ta ɗauka wajen magance matsalar.

Wasu ƴan majalisa na jam’iyyar Republican ne suka gabatar da ƙudirin, wanda a ciki suke kira ga sakataren harkokin wajen Amurka kan ya ayyana wasu ƙungiyoyi ‘yan bindiga a matsayin ‘yan ta’adda, sannan kuma a sanya takunkumi kan wasu ‘yan Nijeriya.

Sauran matakan da ƙudirin ke son a ɗauka su ne hana waɗanda ake zargi da hannu a ‘cin zarafin’ kiristoci shiga Amurka da riƙe kadarorinsu.

Cikin waɗanda sunansu ya fito ɓaro-ɓaro a ƙudirin akwai tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso da ƙungiyar Miyetti Allah Kautal Hore da Miyetti Allah Cattle Breeders (MACBAN) da kuma abin da ƙudirin ya kira “ƙungiyoyin Fulani masu ɗauke da makamai a Nijeriya.”

Ƙudirin, wanda aka yi wa laƙabi da ‘Nigeria Religious Freedom and Accountability Act of 2026’ an gabatar da shi ne da nufin shawo kan zargin da tun farko Amurka ta yi na cewa ana kashe kiristoci a Najeriya kawai saboda addininsu.

Gwamnatin Najeriya dai ta sha musanta zargin musguna wa Kiristoci a ƙasar, inda ta ce “rashin tsaro ya shafi al’umma a ƙasar ba tare da la’akari da bambancin addini ba”.

Tuni dai shugaban Amurka Donald Trump ya ayyana Nijeriya a matsayin ƙasar da ake da damuwa a kanta, wato “country of particular concern”.

By Babaji