
Majalisar zartarwa Ƙungiyar Tarayyar Afrika (AU) ta amince da bai wa Nijeriya kujera ta dindindin a kwamitin gudanarwa na Babban Bankin Afirka (ACB).
Ministan Harkokin Waje na Nijeriya, Yusuf Tuggar ya bayyana cewa matakin na nuna muhimmiyar rawar da Nijeriya ke takawa wajen tsara tsarin kuɗi da tattalin arziƙin Nahiyar Afirka.
A cewarsa, nasarar na daga cikin muhimman abubuwan da Nijeriya ta cimma a zaman taro na 39 na AU, wanda hakan ya ƙara tabbatar da jagorancin ƙasar wajen bunƙasa haɗin kan tattalin arziƙi, zaman lafiya, tsaro da dimukraɗiyya a nahiyar.
Ya kuma ce, wakilcin Nijeriya ya faɗaɗa zuwa kwamitin fasaha na Cibiyar Kuɗi ta Afirka, wanda ke zama matakin farko kafin kafa Babban Bankin na Afirka.
Kazalika, Gwamnatin Tarayya ta jaddada aniyarta ta cigaba da aiki tare da ƙasashen Afirka domin cimma wadata da ci-gaba mai ɗorewa a nahiyar.
