
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Wani ɗan Nijeriya mai suna Abubakar Adamu, ya yi magiya ga Gwamnatin Tarayya da ta gaggauta ɗaukar matakin dawo da shi gida daga ƙasar Rasha bayan da ya zargi cewa an yaudare shi wajen shigar da shi rundunar sojin Rasha da sunan ba shi aikin gadi.
A cewar ƙwararre akan lamuran daƙile ayyukan ta’addanci, Zagazola Makama, tuni lauyoyin Adamu sun sanar da hukumomin Nijeriya halin da yake ciki a Rasha.
Lauyoyin sun bayyana cewa, Adamu ya tafi Moscow ne da bizar yawon buɗe ido wadda Ofishin Jakadancin Rasha da ke Abuja ya ba shi a ranar 16 ga Oktoban 2025, inda aka yi masa alƙawarin sama masa aikin sintiri.
Zuwan sa Rasha ke da wuya, aka ƙwace takardun tafiyarsa tare da tilasta masa sanya hannu akan takardun shiga soja da aka rubuta gaba ɗaya da harshen Rasha, ba tare da an fassara ba.
Daga bisani, Adamu ya gano cewa an shigar da shi cikin rundunar sojin Rasha, wanda a cewar lauyoyin nasa, a halin yanzu yana maƙale a sansanin sojin ƙasar bayan tura shi yankunan yaƙi a Ukraniya.
A ranar Alhamis, Hukumar Leken Asirin Tsaro ta Ukraine ta ce ta gano gawarwakin ’yan Nijeriya biyu a yankin Luhansk, waɗanda ake zargin suna yaƙi a ɓangaren Rasha a yaƙin da ke gudana.
An bayyana sunayen ’yan Nijeriyar da suka mutu a matsayin Hamzat Kazeem Kolawole mai shekaru 42 da Mbah Stephen Udoka mai shekaru 38, waɗanda suka rasu a ƙarshen watan Nuwamba 2025, watanni kaɗan bayan shiga rundunar sojin Rasha.
A wani bincike da CNN ta gudanar kwanan nan, an bayyana yadda ake zargin an yaudari ’yan Afirka daga Ghana, Nijeriya, Kenya da Uganda zuwa Rasha da sunan ba su ayyukan farar hula kamar direbobi ko masu gadi.
Rahoton ya bayyana cewa, da zarar sun isa Rasha, ana zargin an tilasta musu shiga aikin soja tare da ba su ƙarancin horo kafin a tura su sahun gaba.
A ranar Talata, Andrey Podyelyshev, jakadan Rasha a Nijeriya, ya musanta rahotannin tare da nesanta gwamnatin ƙasar daga shirin zambar da ake zargin ta da shi.
