Gwamnatin Katsina ta biya Naira miliyan 500 diyyar faɗaɗa hanyoyi a garin

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Gwamnatin Jihar Katsina ta biya diyyar kudi sama da Naira miliyan 500 ga mutanen da ayyukan faɗaɗa hanyoyi suka shafa a birnin Katsina.

A cewar gwamnati, an biya Naira 469,108,142.68 ga mutane 256 da aikin faɗaɗa hanyar Rafin-daɗi zuwa Batsari mai tsawon kilomita 8 ya shafa.

Haka kuma an biya Naira 21,734,150 ga mutane 22 da aikin filin jirgi zuwa titin da ya zagaye Katsina ta Gabas (Eastern Bypass) mai tsawon kilomita 3.4 ya shafa.

Sannan an biya Naira 40,968,292.50 ga mutane 43 da aikin hanyar Barhim zuwa titin da ya zagaye Katsina ta Gabas (Eastern Bypass) mai tsawon kilomita 3.9 ya shafa.

An kaddamar da rabon cekin kuɗin diyyar ne a ɗakin taro na karamar hukumar Katsina, inda kwamishinan ƙasa da tsare-tsare, Dr. Faisal Umar Kaita, ya jagoranci miƙa cekin ga waɗanda suka amfana.

Da yake jawabi a wajen taron, shugaban ƙaramar hukumar Katsina, Hon. Isah Miqdad AD Saude, ya nuna jin daɗin sa kan ƙoƙarin gwamnatin jihar na fadada hanyoyi tare da biyan wadanda abin ya shafa hakkokinsu, yana mai yabawa da tsare-tsaren raya kasa da ake aiwatarwa a fannoni daban-daban.

A nasa ɓangaren, Dr. Faisal Umar Kaita ya bayyana cewa biyan diyyar kafin aiwatar da manyan ayyuka na nuna yadda gwamnatin jihar ke mutunta hakkin al’umma tare da fifita jin daɗin jama’a.

Ya kuma tabbatar wa da al’umma cewa gwamnatin jihar za ta ci gaba da gudanar da ayyukan raya kasa bisa gaskiya da adalci, tare da hada kai da jama’a domin samun ci gaba mai dorewa a fadin jihar.

By ukarofi