‘Yan bindiga sun kashe DPO a Katsina

Spread the love

Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina

Jami’in hulɗa da jama’a na rundunar ‘yan sanda a Katsina ya sanar da haka a wata takardar sanarwa da ya fitar.

Ya ce lamarin ya faru ne a ƙauyen Magage da ke ƙaramar hukumar Rimi bayan da yan sanda suka sami labarin sirri na ɓullan ‘yan bindigan a ƙauyen.

Na take shugaban yan sandan DPO na ƙaramar hukumar Rimi tare da jami’an sa da sojoji ya jagoranci zuwa ƙauyen na Magage.

Bayan da akayi ta ɗauki ba dadi tsakanin jami’an tsaro da yan bindiga a kauyen, Allah yaba jami’an tsaron sa’ar kuɓutar da dabbobin da yan bindigan sukayi ƙoƙarin sacewa.

Sai da yan bindigan sun harbe shugaban yan sanda da ya jagoranci tawagar jami’an tsaron har lahira tare da harbin wani ɗan sanda a hannu wanda yanzu haka yan asibiti yana samun kulawa.

“Yan sanda kuma sun kashe yan bindiga uku wasu kuma suka gudu suna ɗauke da raunuka.

Kwamishinan yan sanda a jihar Katsina CP Bello Shehu ya jinjiwa jami’an tsaron bisa ƙwarewa da suka nuna inda har ta kai su da ceto dabbobin baki ɗaya.

Haka kuma CP Bello Shehu ya miƙa ta’aziyar sa a madadin rundunar ‘yan sanda na jihar da ƙasa baki ɗaya ga iyalan DPO da ya rasa ransa.

Ya bayyana shugaban “yan sandan da ya rasu a matsayin jarumi,mai gaskiya da nuna ƙwarewa akan aikinsa da fatan Allah masa rahama.

By ukarofi