Hukumar ƙididdiga ta Jihar Kano ta ƙara inganta ayyuka da sahihancin bayanai – Dr. Surajo

Spread the love

Daga RABIU SANUSI a Kano 

Babban Daraktan Hukumar ƙididdiga ta Jihar Kano, Dr. Surajo Sulaiman ya bayyana cewa hukumar ta samu gagarumar sauyi da ci gaba a ‘yan shekarun nan sakamakon gyare-gyare da aka aiwatar da kuma goyon bayan gwamnatin Jihar Kano.

Dr. Surajo ya yaba da irin gagarumin ƙoƙarin da Dr. Aliyu Isah Aliyu ya yi a baya, inda ya ce irin jajircewarsa ta taimaka wajen ɗorar da hukumar kan tubalin inganci da ƙwarewa.

Ya bayyana cewa kimanin shekaru uku da suka gabata aikin a hukumar yana fuskantar ƙalubale, har ma wasu ma’aikata ke kallon tura su aikin a matsayin hukunci.

Sai dai ya ce a halin yanzu lamarin ya sauya, inda ma’aikatan hukumar ke samun kulawa mai kyau ingantaccen yanayin aiki tare da cikakken goyon bayan Gwamna Abba Kabir Yusuf da kuma wasu ƙungiyoyi masu ruwa da tsaki.

Babban Daraktan ya ce hukumar na ƙoƙari matuƙa wajen kare martabar Jihar Kano da al’ummarta ta hanyar samar da sahihan bayanai na ƙididdiga. 

Ya jaddada cewa duk wani bayani da ya shafi ƙididdiga a jihar dole ne ya kasance mai inganci gaskiya da amintacce.

A cewarsa, hukumar ta samar da hanyoyi na zamani da ake tantance sahihancin bayanai kan yawan jama’a da sauran muhimman fannoni a dukkan yankunan jihar, ba tare da la’akari da harshe ko wurin zama ba.

Dr. Surajo ya bayyana cewa hukumar ta aiwatar da ayyuka da dama, ciki har da aikin tattara bayanai kan manyan makarantu a Jihar Kano wani shiri da gwamnati ke gudanarwa a duk shekara domin tsara manufofi.

Ya ƙara da cewa a bana ma mai girma Gwamnan Jihar Kano ya amince da ci gaba da wannan aiki inda ya bayyana cewa nan ba da jimawa ba za a gudanar da taron masu ruwa da tsaki domin ƙara inganta tsarin.

Ya buƙaci duk wanda ke buƙatar bayanan ƙididdiga da ya rubuta takarda kai tsaye zuwa hukumar, inda za a duba buƙatar tare da tantance sahihancinta kafin fitar da bayanan da ake nema.

Daga cikin ayyukan da aka gudanar kwanan nan, hukumar ta yi kididdigar makabartu domin fahimtar adadin mutanen da suka rasu da nufin taimaka wa gwamnati wajen tsara tallafi da shirye-shiryen da za su amfani iyalan da mamata ta bari.

Haka kuma, hukumar na hada kai da hukumomin da abin ya shafa domin gano hanyoyin shigo da miyagun ƙwayoyi a Jihar Kano tare da tantance adadin mutanen da ke shaye-shaye, domin taimaka wa gwamnati wajen ɗaukar matakan daƙile matsalolin tsaro da laifuka da ke da alaƙa da shan miyagun kwayoyi.

Dr. Surajo ya jaddada cewa hukumar na dogaro da bayanai da ra’ayoyin da jama’a ke bayarwa domin magance matsalolinsu da inganta rayuwarsu. Saboda haka ya yi kira ga al’ummar Jihar Kano da su ba ma’aikatan hukumar cikakken hadin kai yayin ayyukan tattara bayanai, domin samun ci gaba mai ɗorewa.

By ukarofi