Daga RABIU SANUSI a Kano
Yayin da watan Ramadan mai alfarma ke ƙaratowa, Hukumar Kula da Jin Daɗin Al’umma ta Jihar Kano (KASPA) ta yi kira ga attire, kamfanoni masu zaman kansu da kuma ƙungiyoyi masu zaman kansu (NGOs) da su tallafa wa sama da mutane miliyan 1.7 masu rauni da karancin hali da ke cikin kundin bayanan hukumar a faɗin jihar.
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Daraktan Wayar da Kan Jama’a na KASPA Rabiu Abubakar Kura, ya fitar kuma ya bai wa manema labarai.
Sanarwar ta bayyana cewa Daraktar Janar ta KASPA Dakta Fateema Abubakar Abdullahi (Amneef), ce ta yi wannan kira yayin wani taron shugabanni da aka gudanar a hedikwatar hukumar.
Dakta Fateema ta bayyana cewa ga iyalai da dama a Jihar Kano watan Ramadan na zuwa ne da manyan ƙalubale inda talauci da hauhawar farashin kayayyaki ke sanya wahala wajen samun muhimman abubuwan rayuwa kamar abinci da kiwon lafiya.
Ta jaddada buƙatar haɗin kai, tausayi da ɗaukar nauyin juna domin rage radadin da talakawa da masu rauni ke fuskanta, musamman a wannan wata mai tsarki da ake koyar da kyautatawa da kulawa da juna.
Daraktar Janar ta yabawa Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, bisa jajircewarsa wajen kula da jin daɗin al’umma musamman shirin ciyar da jama’a na Ramadan da gwamnatin jihar ke aiwatarwa, wanda ta ce ya zamo abin sauƙi da fata ga dubban gidaje masu fama da ƙunci.
Haka kuma ta bayyana shirin kiwon lafiya kyauta na KASPA/KACHMA, wanda a halin yanzu ke ba da tallafin lafiya ga fiye da marayu da tsofaffi 20,000 a faɗin Jihar Kano da dama daga cikinsu ba za su iya samun irin wannan kulawa ba da kansu.
A cewarta, bayar da tallafi a watan Ramadan ba wai aikin sadaka kaɗai ba ne, illa wajibi ne na ɗabi’a domin kare mutuncin bil’adama da kuma kula da mafi rauni a cikin al’umma.
Ta kuma yi kira ga duk masu niyyar tallafa wa ko cin gajiyar shirye-shiryen KASPA da su tuntuɓi hukumar domin ƙarin haɗin gwiwa.
Dakta Fateema ta sake jaddada ƙudurin KASPA na ƙarfafa tsare-tsaren kariyar al’umma da tabbatar da cewa babu wani ɗan ƙasa mai rauni da za a bari a baya, musamman a irin wannan lokaci mai muhimmanci na watan Ramadan.
