Majalisar Dattawa ta amince da watsa sakamakon zaɓe kai tsaye ta intanet

Spread the love

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Majalisar Dattawa a ranar Litinin ta yi mi’ara koma baya kan matakin da ta ɗauka kan gyaran dokar zaɓe bayan da ta yi watsi da buƙatar tilasta tura sakamakon zaɓe kai tsaye ta intanet daga rumfunan zaɓe zuwa ga shafin hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (IREɓ) bayan an ƙirga ƙuri’u.

Majalisar tana aikin sake gyara dokar zaɓen ne domin shigar da tanadin tura sakamakon zaɓe kai tsaye ta intanet. Sai dai a yayin da aka samu gazawar intanet, za a yi amfani da takardar rubuta sakamakon zaɓena EC8A a matsayin hanyar tura sakamakon zaɓe.

Duk da wannan canji, gyran dokar bai ayyana tura sakamakon zaben kai tsaye a matsayin wajibi ba. A maimakon haka, ta yarda da tura sakamakon zaɓen ta intanet ne tare da ba da zaɓi idan aka rasa intanet.

Wannan mataki ya biyo bayan ƙudurin da mai tsawatarwa a majalisar Tahir Monguno, ya gabatar kan zaman na gaggawa.

Monguno wanda ke wakiltar Borno ta Arewa, ya ce wannan mataki na mi’ara koma baya na zuwa ne bayan ƙin amincewa da majalisar ta yi da ƙudurin tura sakamakon zaɓe kai tsaye ta inatanet saɓanin muradin al’ummar Nijeriya.

“Wannan gyara an yi shi ne domin dacewa da muradan al’umma. Ni ne na gabatar da ƙuduri kan ci gaba da amfani da dokar zaɓe wadda ta jawo ka-ce-na-ce,” ya bayyana.

A yayin duba dokar saɗara-saɗara a ranar Larabar da ta gaba, Monguno ya buƙaci majalisar da ta ci gaba da amfani da tanadin sashen doka ta 60 ta kundin dokar zaɓen 2022 wanda ya amince da tura sakamakon zaɓe zuwa cibiyoyin tattara sakamakon zaɓe.

Sai dai a zamanta na ranar Talata, Monguno ya yi mi’ara koma baya inda ya buƙaci majalisar da ta soke matakin da ta ɗauka na farko saboda ka-ce-na-ce da ya jawo.

Ya ce, sasshen ya buƙaci a samu kyakkyawan tsarin da zai tabbatar da an yi zaɓe yadda ya kamata kuma a buɗe.

“Bayan duba dokar a saosia, sai wasu abubuwa sun taso kan sashe na 60(3) wanda ya buƙaci majalisar ta sake dubawa domin tabbatar da an gudanar da sahihin zaɓe cikin kwanciyar hankali a buɗe a Nijeriya .”

Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya mara wa ƙudurin baya ta hanyar tura saƙon murya.

Amincewa da sabuwar dokar da majalisa ta yi na nufin ta yarda da tanadin dokar na farko wanda bai yi magana game da aika sakamakon zaɓe kai tsaye ba ta intanet.

Sai dai tun ranar Alhamis ɗin da ta gabata ne ‘yan Nijeriya  ke ta muhawara a kan gyaran dokar zaɓen da majalisa ta yi a ranar Laraba.

Duk da cewa an gyara dokoki da yawa da suka shafi zaben, amma hankalin al’umma ya fi karkata ne kan waccan wadda ta shafi ƙin amincewa da tura sakamakon zaɓe kai tsaye ta intanet daga rumfunan zaɓe zuwa ga matattarar bayanan INEC ta IREɓ.

Ra’ayin al’umma ta rabu gida biyu, sai dai, jam’iyyu da yawa siyasa da dama da masu amfani da kafafen sada zumunta sun yi watsi da matsayin da majalisar ta ɗauka tare da neman ta sake duba matsayinta.

Wasu daga cikin ‘yan siyasa da ƙungiyoyin al’umma da masu rajin kare haƙƙin al’umma sun gudanar da zanga-zanga a ƙofara majalisar dattawa suna neman lallai ne a shigar da tanadin tura sakamakon zaɓen kai tsaye ta intanet cikin dokar zaɓe.

ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen shekarar 2023, Peter Obi, ya jagoranci mutane domin yin zanga-zanga a ranar Litinin.

Tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi; da tsohon ministan matasa da bunƙasa wasanni, Simon Dalung; da mai fafutukar kare haƙkin al’umma kuma mamallakin jaridar Sahara Reporters, Omoyele Sowore, sun jagoranci zanga-zanaga a ranar Talata.

Kafin fara zanga-zangar a ranar Litinin, wasu daga cikin sanatoci daga kungiyarsu ta marasa rinjaye sun gana da manema labarai a ranar Alhamis inda suka ce tuni aka shigar da tanadin tura sakamakon zaɓe kai tsaye ta intanet.

‘Yan majalisar a ƙarƙashin sanatan yankin Abia ta Kudu, Eyinnaya Abaribe daga jam’iyyar APGA ya ce, ka-ce-na-cen da ake yi ya samo asali ne daga hira ta gefe da aka riƙa yi a lokacin duba dokar a majalisa.

Haka kuma a yayin ƙaddamar da littafi a ranar Asabar, Akpabio, ya amince cewa ‘yan majalisa suna sane suka cire tanadin aika sakamakon zaɓen kai tsaye a lokacin duba dokar zaɓen.

Akpabio ya yi bayanin cewa matakin na zuwa ne bayan da wasu ‘yan majalisa suka koka kan za a sha dambarwar shari’a idan aka ce an samu matsalar netwok wajen tura sakamakon zaben.

Biyo bayan amincewar majalisar kan gyaran dokar zaɓen, Akpabio, an sake kafa kawamitin tatattara da daidata ra’ayoyi domin magance bambance-bambancen da ake da ita na nau’in ƙudurin biyu na majalisar dattawa da wakilai.

An naɗa Simon Lalong (APC, Filato ta Kudu) a matsayin shugaban kwamitin.

Sauran mambobi sun haɗa da: Tahir Monguno (APC, Borno ta Arewa) da Adamu Aleiro (APC Kebbi ta tsakiya) da Adeniyi Adegbonmire (APC, Ondo ta tsakiya)

Haka kuma akwai sauran mambobi da suka haɗa da: Orji Kalu (APC, Abia ta Kudu) Abba Moro (PDP, Benuwai) da Asuƙuo Ekpeyong (APC, Kuros Ribas) da Aminu Abbas (PDP, Adamawa) da Tokunbo Abiru (APC, Lagos) da Isah Jibrin (APC, Kogi) da Ipalibo Banigo (PDP, Riɓers) da Peter Nwebonyi (APC, Ebonyi).

By ukarofi