Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja
Dubun wani mutum ta cika bayan da ya damfari wata mata kuɗi Naira miliyan 603.4 da cewa zai sa Shugaban ƙasa ya naɗa ta a matsayin Shugabar Kamfanin Mai na ƙasa NNPCL.
Bayan karɓar kuɗin, mutumin tare da wata abokiyar cin mushensa sun yaudari matar gabatar mata da takarda daga Fadar Shugaban ƙasa ta hannun Ofishin Mashawarcin Shugaban ƙasa a fannin Tsaro a matsayin shaidar naɗinta a matsayin shugabar NNPCL.
A ranar Litinin Hukumar Yaƙi da Masu Karya Tattalin Arzikin ƙasa (EFCC) ta gurfanar da mutumin a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke yankin Maitama a Abuja, kan zargin aikata laifuka shida masu alaƙa da damfara.
Lauyan EFCC, Y. Tarfa, ya shaida wa alkali cewa mutumin mai suna Gidado Ibrahim tare da wata mai suna Halimat Adenike Tejusho wadda yanzu ake nema ne suka haɗa baki suka karɓi kudaden da yawansu ya kai Naira miliyan 603,4000,0000 a hannun wata mai suna Oluseye Yomi-Sholoye, da sunan za su sa a nada ta a kujerar Babban Shugaban NNPCL.
Ya ce waɗanda ake zargin sun karbi kudaden ne a cikin wata biyu—watan Agusta zuwa Oktoban shekarar 2024—a matsayin kafin alkalami, inda suka gabatar wa Yomi-Sholoye takardar bugi daga Ofishin Mashawarcin Shugaban Kasa a fannin Tsaro game da nadin ta.
Sai dai bayan karanta masa tuhume-tuhumen, wanda ake zargi ya musanta, inda lauyan EFFCC, Tarfa ta bukaci kotun ta sanya ranar sauraron shari’ar da kuma bayar da umarnin tsare wanda ake zargin a gidan gyaran hali.
Lauyan wanda ake zargi, B. B Alhaji ya sanar da kotun game da bukatar beli da ya shiga, yana mai cewa duk da cewa lokacin sauraron bukatar bai yi ba, yana rokon a tsare wanda yake ƙarewan a ofishin EFCC maimakon gidan yari.
A ƙarshe alƙalin kotun, Mai Sharia Muazu ya dage sauraron karar zuwa ranar 17 ga watan nan na Fabarairu, tare umarnin tsare wanda ake zargin a Gidan Yarin Kuje.
