INEC ta yi wa Atiku martani kan tsokacin jaddawalin zaɓen 2027

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta yi alƙawarin tabbatar wa kowane ɗan ƙasa da ya cancanta ya samu damar yin zaɓe bisa gaskiya da adalci, yayin da ake ƙara tunkarar babban zaɓen 2027.

A ranar Juma’a Farfesa Joash Amupitan, wato Shugaban INEC ya sanar da haka a taron manema labarai a Abuja, inda ya ce za a yi na shugaban ƙasa da ‘yan majalisar dokokin ƙasa a ranar 20 ga Fabrairun 2027, sannan na gwamnoni da ‘yan majalisun jihohi a ranar 6 ga Maris, 2027.

A cewarsa, sun ayyana lokutan ne bisa la’akari da hukunce-hukuncen doka na 1999, ba da wata manufa ta matswa wa wani ɓangare na al’ummar ƙasa ba.

Saidai al’ummar Nijeriya musamman Musulumi sun koka game da ranakun zaɓukan duba da cewa sun daidai da lokacin azumin watan Ramadana, wanda za a fara 8 ga Fabarairu, sannan a kammala a 10 ga Maris, 2027.

Akan haka ne tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ya nemi hukumar da ta sake nazari akan sanya 20 ga Fabarairu a matsayin lokacin zaɓe, saboda hakan zai dace a lokacin da Musulmi ke tsaka da azumi.

A cewar Atiku ta kafar X, lokacin Ramadana yanayi ne na musamman na azumi, tunani da wasu ayyukan ibada ga Musulmin Nijeriya masu yawa.

By Babaji