NDLEA ta cafke ɗan kasuwa a Kano yana yunƙurin safarar hodar iblis zuwa Chana

Spread the love

Hukumar Hana Sha da Fataucin Miyagun ƙwayoyi ta ƙasa (NDLEA), ta cafke wani ɗan kasuwa mai shekaru 62 da ke zaune a Legas bisa zargin yunƙurin safarar hodar iblis zuwa ƙasar Chana ta filin jirgin saman Mallam Aminu Kano da ke jihar Kano.

A wata sanarwa da Daraktan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai na NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar daga hedikwatar hukumar da ke Abuja, ya ce an kama mutumin ne a ranar Asabar yayin tantance fasinjojin da ke shirin tafiya Addis Ababa ta jirgin Ethiopian Airlines, mai lamba ET940, daga nan zuwa Chana.

Binciken da aka yi masa ta hanyar na’urar duba jiki ya nuna cewa ya haɗiye miyagun ƙwayoyi. An tsare shi domin kulawar likitoci, inda daga bisani ya fitar da ƙunshi-ƙunshi 95 na hodar iblis masu girman gaske, da nauyin kilo 1.589, sau bakwai.

A cewar NDLEA, wanda ake zargin ya shaida wa masu bincike cewa yana harkar sayar da kaya da sassan gyaran motoci a Legas, kuma ya tsunduma cikin fataucin ne domin samun kuɗin kammala ginin gida a garinsu Iwollo, jihar Enugu.

Baya ga wannan kamen, NDLEA ta ce ta samu gagarumar nasara a wasu sassa na ƙasar. A Babban Birnin Tarayya, jami’an hukumar sun gano kilo 627.7 na tabar wiwi nau’in skunk a wani ma’aji da ke Kubwa.

Haka kuma, an dakile yunƙurin safarar methamphetamine da aka ɓoye cikin lasifikar MP3 daga Enugu zuwa Abuja da Kaduna. Binciken da ya biyo baya ya kai ga kama wasu da ake zargi a Zuba da Kaduna tare da ƙwato giram 173 da giram 28 na miyagun ƙwayoyin.

A jihar Taraba, an kama wani mutum mai shekaru 32 dauke da kilo 1.8 na methamphetamine da aka ɓoye cikin kwalayen madarar Hollandia a hanyar Dan-Anacha. A Oyo kuwa, an cafke wani ɗan asalin Jamhuriyar Benin da kilo 149.6 na skunk, yayin da a Ibadan aka kama wani da allurai 10,820 na pentazocine da kwayoyi 117,820 na tramadol.

Haka zalika, a Kwara an gano kapsul 395,400 na tramadol da aka ɓoye cikin tankar mai daga Legas zuwa Maiduguri. A Imo, an kama ma’aurata da kilo 203 na skunk, yayin da a Ondo aka gano kilo 420 a wani daji.

A Legas, rundunar ruwa ta NDLEA ta ƙwato kunshe 31 na cocaine daga hannun wani da ya iso daga Cote d’Iɓoire ta ruwa a Badagry. Sauran kamen sun haɗa da masu safarar Canadian Loud, Colorado da sauran ƙwayoyi a Legas da Enugu.

Hukumar NDLEA ta jaddada aniyarta na ƙara matsa lamba kan masu fataucin miyagun ƙwayoyi tare da tabbatar da cewa za a gurfanar da duk wanda aka samu da hannu a gaban kotu.

By ukarofi