Nasarawa 2027: Al’ummar Fulani sun yi alƙawarin yi wa Sanata Wadada ruwan ƙuri’u

Spread the love

DAGA JOHN DOGO WADA, Keffi

A yayin da ake cigaba da shirye-shiryen zaɓukan shekarar 2027 dake tafe, al’ummar Fulani a jihar Nasarawa sunyi alƙawarin mara wa jam’iyyar APC mai ci a jihar baya a zaben 2027 ɗin inda duk suka bayyana cewa suna tare da shugaba ƙasa Bola Ahmed Tinubu da gwanmnan jihar Injiniya Abdullahi Sule da kuma uwa uba Sanata Ahmed Aliyu Wadada wato ɗan takarar kujerar gwamnan jihar a 2027 kenan ɗari bisa ɗari.

Al’ummar Fulanin sun bayyana haka ne a jawabansu ɗaya bayan ɗaya a wajen wani babban taron ƙaddamar da sabbin shugabannin su na ƙungiyar nan da ake kira Miyyeti Allah Kautal hore reshin ƙaramar hukumar Kokona wadda aka gudanar a jiya Lahadi a yankin garin Sabon Gida.

Sun ce sun yanke shawarar mara wa shugabannin uku baya ne a 2027 musamman sanata Ahmed Aliyu Wadada bisa ayyukan cigaba da ya daɗe yana gudanarwa a yankin Kokonan da jihar Nasarawa baki ɗaya waɗanda galibin al’ummar nasu na Fulani ke amfana matuƙa kawo yanzu.

A cewarsu a yanzu haka sun riga sun tantance duka ‘yan takaran gwamnan jihar inda suka gano cewar sanata Ahmed Aliyu Wadada ne yafi cancanta su bashi ƙuri’unsu kana dukansu da suka yi jawabin sun kuma yi kira ga sauran mutanen su da basu samu damar halatar taron ba su tabbatar sun fito ƙwansu da kwarkwata su ma don ayi wa Sanata Wadada ruwan ƙuri’u a lokacin zaɓen.

A nasa ɓangaren da yake jawabi a matsayin babban baƙo na musamman, sanatan mai wakiltar mazaɓar Nasarawa ta Yamma, Ahmed Aliyu Wadada ya godewa al’ummar Fulanin dana gane da mataki da duk suka ɗauka na bayyana cewa suna tare da shugaba Tinubu da gwamnan Sule da kuma shi kansa, yana mai cewa shugaban ƙasar Tinubu na da niyyar gyara ƙasarnan kuma yana yi a yanzu sannan shima gwanmna Sule na da kishin cigaban jihar shiyasa yake aiki fiye da misali don bunƙasa duka fannonin jihar.

Wadada ya ƙara da cewa wannan tarin mutanen Fulani da sauran jama’a ta nuna cewa sun yarda da shi cewa shi kaɗai ne zai iya samu musu ribobin dimokraɗiyya ya ɗaura daga inda gwamna Sule zai tsaya a 2027.

Daga nan sai Sanata Ahmed Aliyu Wadada ya kuma yi amfani da damar inda ya roƙe waɗanda ke da galihu su rika tallafa wa ƙoƙarin shugaba Tinubu da gwanmna Sule don ɗorewar cigaba da ake samu a yanzu inda ya kuma yi alƙawarin cigaba da inganta harkokin al’ummar sa na shiyar da jihar baki ɗaya musamman idan ya zama gwamnan jihar ta Nasarawa a 2027.

Sauran abubuwa da aka gudanar a wajen taron sun haɗa da ƙaddamar da sabbin shugabannin ƙungiyar Miyyeti Allah Kautal hore reshen ƙaramar hukumar Kokona ɗin da sauran su.

Wakilin mu a jihar ta Nasarawa John D. Wada ya kuma rawaito cewa a yanzu haka Sanata Aliyu Wadada ne yafi samun yawan magoya baya daga cikin duka ‘yan takaran kujerar gwamnan jihar ta Nasarawa inda ɗimbin mutane daga sassan jihar ke cigaba da fito fili suna bayyana goyon bayan su wa sanatan.

By ukarofi