
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
An samu ɓarkewar hatsaniya a harabar Hedikwatar Hukumar Yaƙi da yi wa Tattalin Arziƙin Ƙasa Ta’annati (EFCC) da ke Abuja a lokacin da magoya baya da masu adawa da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufa’i suka yi arangama yayin da ya je ofishin hukumar.
Wannan al’amari ya tilasta wa jami’an tsaro harba hayaƙi mai sa hawaye domin tarwatsa dandazon jama’ar.
Shaidun gani da ido sun ce, rikicin ya fara ne bayan da ɓangarorin biyu suka fara musayar kalamai a harabar, inda masu goyon bayan bincike akan El-Rufai ke rera taken “El-Rufa’i bai fi ƙarfin doka ba” da kuma “a bar doka ta yi aikinta.”
Rahotanni sun bayyana cewa, El-Rufa’i ya isa ofishin ne da safe, inda ya shiga domin ganawa da jami’an binciken a yau Litinin, 16 ga Fabrairu, wadda rana ce ta zagayowar haihuwarsa.
Saidai, har yanzu ba a bayyana cikakken bayani kan dalilin gayyatar ba, amma ana zargin yana da alaƙa da wasu batutuwan gudanarwa a lokacin mulkinsa da wssu muhimman lamuran ƙasa.
Haka kuma, jami’an hukumar ba su fitar da wata sanarwa kai tsaye akan lamarin ba, sai dai an tabbatar da cewa ana ci gaba da bincike bisa doka.
Kazalika, zanga-zangar ta kasance cikin lumana, tare da sa ido daga jami’an tsaro domin kauce wa duk wata hargitsi da ka iya zama barazana ga zaman lafiyar al’umma.
