Daga ABDULLAHI MUHAMMAD a Katsina
Wannan wutar lantarkin na ɗaya daga cikin aikin mazaɓu da tsohon Sanata Bello Mandiya ya kawo a babban asibitin.
Shugaban ƙungiyar cigaban Funtua kwamred Mannir Suleiman ya sanar da haka a wata hira da manema labarai a Katsina.
Ya ce tunda na’urar ta tsaya shekara bakwai da suka wuce har yanzu babu wanda ya waiwaiyi aikin.
Haka kuma kwamred Suleiman ya bayyana cewa babban na’urar samar da wutar lantarki (Generator) shima tuni ya bar aiki a asibitin.
Ya bayyana cewa marasa lafiya na ƙananan hukumomin da ke maƙwabtaka da Funtua ke tururuwa zuwa asibitin neman magani.
Kwamred Suleiman ya ce waɗannan na’urorin wutar lantarki na taimakawa sosai kasancewa ba kasafai ake samun wutar lantarki daga KEDCO ba.
Sai ya yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su wa Allah su duba lamarin domin ceto rayukan al’ummar mutanen yankin.
Ya jinjina wa Gwamna Dikko Raɗɗa kan yadda ya tashi tsaye wajen bunƙasa harkokin lafiya a jihar.
“Dikko ya gina manyan asibitoci a faɗin jihar tare da samar masu da na’urorin gwaji da bincike na zamani”,inji Mannir.
Shugaban ƙungiyar harwala yau ya yabi kwamishinan harkokin lafiya Hon Musa Adamu Funtua kan yadda ya ke tsabtace makarantun kiwon lafiya masu zaman kansu da yace a yanzu makarantun sun daidaita da sauran takwarorin su na wasu jihohi.
